Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Har yanzu PSG ba ta haƙura da Mbappe ba, Chelsea za ta rabu da 'yan wasa biyu
Har yanzu kociyan Paris St-Germain Luis Enrique na fatan shawo kan Kylian Mbappe, ya zauna maimakon tafiya Real Madrid idan kwantiraginsa ya kare a karshen kaka. (Goal)
Chelsea na shirin sayar da 'yan wasanta biyu na tawagar Ingila - dan baya Reece James, da dan tsakiya Conor Gallagher, a bazaran nan domin kauce wa saba dokokin hukumar gasar Premier na kudi. (Times )
West Ham na dab da kammala sayen danwasan Brentford da Ingila Ivan Toney, kamar yadda kungiyar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar. (Football Insider)
Kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce bai damu ba a kan jita-jitar da ake yi cewa Vinicius Jr zai bar kungiyar saboda cin mutuncinsa da ake yi na wariyar launin fata.(Diario Sport)
Ruben Amorim ya ce hankalinsa na nan daram a kan Sporting Lisbon da kuma cin kofuna da kungiyar yayin da ake jita-jitar cewa shi zai maye gurbin Jurgen Klopp a Liverpool. (Star)
Kociyan Getafe Jose Bordalas ya ce har yanzu bai san abin da ake ciki ba a game da makomar Mason Greenwood a kungiyar, saboda har yanzu Manchester United ba ta ce komai ba a kan komar danwasan. (Manchester Evening News)
Sporting Lisbon tana son fam miliyan 68.5 a kan dan-wasanta mai kai hari Viktor Gyokeres, dan Sweden wanda ke kan ganiyarsa, sakamakon sha'awarsa da Arsenal da Chelsea ke yi. (Sunday Mirror)
Bayern Munich ta tabbatar dan-wasanta na tsakiya Joshua Kimmich, dan Jamus ba zai tsawaita kwantiraginsa a kungiyar ba, har sai ta samu sabon kociyan da zai maye gurbin Thomas Tuchel, wanda zai tafi a karshen kaka. (Sky Germany, daga 90min)
Barcelona da Chelsea sun dukufa wajen zawarcin matashin dan-wasan Brazil na Palmeiras Estevao Willian, mai shekara 16, wanda kudin sakinsa aka ce ya kai fam miliyan 51. (Sunday Mirror)