Guinea Bissau ta ci Super Eagles a Najeriya

Asalin hoton, Super Eagles
Tawagar Nageriya ta yi rashin nasara a hannun Guinea Bissau da ci 1-0 a wasan neman shiga kofin Afirka da suka buga a Abuja, ranar Juma'a.
Wasa ne na uku-uku a rukunin farko don neman gurbin shiga babbar gasar kwallon kafa ta Afira da za a yi a Ivory Coast a 2024.
Guinea Bissau ta ci kwallon ta hannun Tanguy Zoukrou a minti na 29 da fara wasa a karawar da suka yi a filin wasa na Moshood Abiola a Abuja, Nageria.
Da wannan sakamakon Guinea Bissau ta koma ta daya a rukunin farko da maki bakwai, bayan da ta ci Super Eagles da cin Sao Tome da canjaras da Saliyo.
Super Eagles ta koma ta biyu da maki shida, bayan nasara a kan Saliyo da Sao Tome.
Ranar Laraba Saliyo da Sao Tome suka tashi wasa 2-2 a daya karawa ta uku a rukunin farko.
Ranar Litinin 27 ga watan Maris Super Eagles za ta ziyarci Guinea Bissau, domin buga wasa na hur-hudu a rukunin farko.
Ita kuwa Sao Tome za ta karbi bakuncin Saliyo ranar Lahadi 26 ga watan Maris.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jerin 'yan wasan da Najeriya ta gayyata:
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Victor Sochima (Rivers United); Kingsley Aniagboso (Giant Brillars)
Masu tsaron baya: Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Calvin Bassey (FC Ajax, The Netherlands); Daniel Bameyi (YumYum FC); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal)
Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Everton FC, England); Joe Aribo (Southampton, England)
Masu cin kwallaye: Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Ahmed Musa (Sivasspor K, Turkey); Samuel Chukwueze (Villarreal CF, Spain); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta BC, Italy); Terem Moffi (OGC Nice, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Paul Onuachu (Southampton FC, England)











