‘Yan bindiga 'suna ci gaba da tarwatsa kauyukan Zamfara'

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
An wallafa

Matsalar hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da addabar kauyuka da dama na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

 

Hare-hare na baya-bayan nan sun tilasta wa jama'a tserewa daga garuruwansu, lamarin da ya gurgunta harkar noma a yankin karamar hukumar Gumi, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana wa BBC Hausa.

 

Daya daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari shi ne kudancin karamar hukumar Gumi.

 

Wani mazaunin yankin ya ce "Tun bayan kammala hidimar Sallah manoma ba su iya gudanar da ayyukansu, guje-guje kawai muke yi.”

Ya ce a yanzu haka kusan dukkanin mutanen yankin sun tsere zuwa cibiyar karamar hukumar.

 

Ya kara da cewa bayan kashe mutane, 'yan bindigar sun kuma sace dabbobi wadanda ba za a iya kiyasta yawansu ba.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .

"Garin Kangon Garekki na karamar hukumar Maru ma na cikin mawuyacin yanayi", in ji wani mutumin yankin.

 

Ya ce "Da misalin karfe 9 na dare suka fado wa mutane suna ta harbi, suka kashe mutum shida, am kuma kai mutum 3 asibiti.”

 

Ya dai tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba duk kuwa da cewa na yi wani zaman sasantawa da ‘yan fashin a ranar Talata.

Sai dai ya ce jami’na tsaron da ke a kauyen sun yi kokari inda suka kori maharan kafin su ci gaba da barna.

‘Idan ba za a iya yakar su ba a yi sulhu’

Mutumin kauyen da ke a yankin Gumi ya ce a shekarun baya an samu sassaucin hare-haren bayan da aka yi sulhu tsakanin mutanen kauyukan da 'yan bindigan.

 

Sai dai a cewar sa lamarin ya sake kazancewa a baya-bayan nan.

 

Amma ya yi kira ga gwamnati cewa "Muna kira ga shugaban kasa ya taimaka, mutanen nan idan ba a iya yakar su, a yi kokari a yi sulhu da su saboda a zauna lafiya.”

 

Shi kuwa mutumin Kangon Garekki cewa ya yi ya kamata gwamnati ta yi kokarin koran ‘yan bindiga daga yankin nasu ta yadda za su iya gudanar da noma domin samun abinci.

Ya ce "Abin da muke so shi ne gwamnati ta taimake mu ta shiga tsakaninmu da wadannan mutane saboda mu koma garuruwanmu mu ci gaba da noma domin mu samu abin da za mu ciyar da iyalanmu.”