Yadda matsalar daba ke ci gaba da zama ƙarfen-ƙafa a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da suka fi fama da matsalar rashin tsaro da ta haɗa da hare-haren ƴan fashin daji.
Sai dai wata matsala da ta ƙara kunno kai a babban birnin jihar, wato Gusau, ita ce ta ƙaruwar ayyukan matasa ƴan Sara-Suka’, da ke ƙwacen wayoyin salula, a wasu lokuta ma su illata mutanen da suka haɗu da ɓacin rana.
Wakilin BBC, Jabir Mustapha Sambo, ya je birnin na Gusau, kuma ya duba mana yadda girman wannan matsala yake.
BBC ta tattauna da wani wanda ya taɓa fuskantar matsalar ƴan sara-sukar inda ya ce "yaron sai ya ruga ya tare ni a gaba, sai ya daka min wuƙa a ciki, Allah Ya sa wuƙar ba ta shiga ciki ba, ta dan yanke ni kaɗan.
"Allah Ya kawo wani mutum, ya riƙe su sai suka ture shi, kawai sai na ji wukar a goshina, sai na riƙe ta, amma suka ja, sai faratana uku suka samu matsala”.
Wani kuma da ya taɓa ganewa idonsa irin wannan hari yayin wani bikin al'ada na Fulani da ake kira Sharo, ya shaida wa BBC yadda aka yi wa masu irin wannan aika-aika duka inda daga bisani suka tare wata hanya suka auka wa wasu matasa uku a kan babur har ta kai ga asarar rai.
Me hukumomi suke yi?
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar ta Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce matsalar tana da girma ganin yadda ƙananan yara suke riƙe manya-manyan makamai - adda da wuƙaƙe.
"A ce ba ka da ikon ka rike wayarka, ba ka da ikon ka shiga wata unguwa, sai an kawo maka hari?" in ji SP Shehu.
Sai dai ya ce tun bayan da suka ƙaddamar da samamen yaƙi da ayyukan matasan da ke daba, da yawansu an kama su, wasu kuma an kai su kotu, wasu kuma an tura su gidajen yari.
Wani abin damuwa ga al'ummar wannan birni na Gusau shi ne yadda ake ci gaba da fuskantar ƙaruwar wannan matsala ganin yadda zaɓen 2023 ke tafe da zargin wasu ƴan siyasa da amfani da matasan wajen cimma buƙatunsu.











