Mazauna Zamfara na cikin juyayi bayan sace mutum 40 yayin Sallar Juma'a

An wallafa

Mazauna garin Zugu na Ƙaramar Hukumar Bukuyum a Jihar Zamfara sun wuni cikin tashin hankali bayan 'yan fashi ɗauke da mugayen makamai sun kutsa masallacin Juma'a 'yan mintuna kafin tayar da sallar.

Bayanan da BBC Hausa ta tattara sun nuna cewa maharan sun shiga masallacin tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 1:30 na rana kuma suka yi awon gaba da mutane da dama.

Kazalika, sun wuce zuwa kasuwar da ke garin inda a nan ma suka tafi da wasu. Jimilla, mutum aƙalla 44 ake zaton sun sace.

Wani mazaunin yankin ya ce baya ga mutanen da suka sace, 'yan fashin sun kuma ɗebi kayayyakin abinci da sauran abubuwa.

Rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce ba ta da haƙiƙanin adadin mutanen da aka sace ɗin.

"Sun ɗebi kayan abinci kamar biredi da wayoyin mutane da batira," in ji shi.

Ya ƙara da cewa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu wani bayani da suka samu daga jami'an tsaro ko kuma 'yan bindigar.

'Karo na huɗu ke nan'

Wasu mazauna yankin sun ce mutanen sun ɓoye bindigogin ne a cikin rigunansu kafin su shiga masallacin a daidai lokacin da liman ke ƙoƙarin fara huɗubar Juma'a.

An ce har sai da suka umarci waɗanda ke harabar masallacin da su kom ciki.

Wani mutum da muka ɓoye sunansa saboda dalilai na tsaro ya ce da ma 'yan fashin sun saba shiga garin don aikata fashi.

"Sun sha shigowa, wannan ne karo na huɗu," a cewarsa. "Bayan sun tafi da su jami'an tsaro sun zo amma ba su ɗauki wani dogon lokaci ba suka tafi."

Kazalika, wata majiya daban ta ce 'yan bindigar sun faɗa wa masu ibadar cewa sun je ne domin tattauna sakin wasu mutane da aka kama.

"Babu wanda ya ga bindigogin nasu da gfarko, shi ya sa wasu suka zaci su ma masu sallah ne kawai. Amma suna shiga cikin masallaci sai suka fito da su kuma suka yi harbin gargaɗi.

"Wasu daga cikin masallata sun tsere ta tagogin masallacin, amma sun tafi da wasu cikin daji."

Yanzu haka mazauna yankin na cikin juyayi yayin da wasu da yawa suka gudu, a cewar majiyar.