Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wani mutum ya halaka iyayensa da taɓarya a Jigawa
Rundunar ƴan sanda ta Najeriya ta ce ta cafke Munkaila Ahmadu mai shekara 37 da ya yi amfani da taɓarya wajen halaka iyayensa a jihar Jigawa a arewacin Najeriya.
Iyayen - Ahmad Muhammad ɗai shekara 70 wanda mai unguwar Zarada Sabuwa da mai ɗakinsa Hauwa'u Ahmadu mai shekara 60.
Wasu mutum biyu sun ji rauni a lamarin yayin da Munkaila ya yi amfani da taɓarya wajen lakaɗa musu duka kuma suna samun kulawa a babban asibitin Gumel da ke Jigawa.
Babu ƙarin bayani kan abin da ya sa ake zargin Munkaila da aikata haka amma mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya faɗa wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa Munkaila na cikin ƙoshin lafiya kuma ba ya ta'amali da ƙwaya.
"A ranar 1 ga watan Satumbar 2022 kimanin ƙarfe 11:30 mun samu rahoton cewa wani Munkaila Ahmadu mai shekara 37 ya kai wa wasu hari da taɓarya."
"Jami'anmu sun garzaya wajen tare da kai mutane huɗu zuwa babban asibitin Gumel inda likitoci suka tabbatar da mutuwar Ahmad Muhammad mai shekara 70 da mai ɗakinsa Hauwa'u Ahmadu mai shekara 60, iyayen Munkaila da ya tafka aika-aikar.
"Mutanen biyu da suka ji rauni Hakalima Ahmadu ta kasance abokiyar zaman Munkaila yayin da Kailu Bagudu kuma maƙoci ne da ya yi ƙoƙarin shiga tsakani a lokacin da aka kai harin.
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sanda ya ba da umarnin a mayar da Munkaila sashen binciken manyan laifuka domin a duba lamarin.
End of Wasu labarai masu alaƙa
Ko a watan da ya gabata ma, ƴan sanda a Katsina sun kama Najib Shehu mai shekara 25 wanda ya yi amfani da taɓarya wajen zane abokiyar zaman mahaifiyarsa har ya kai ga mutuwarta tare da raunata mahaifinsa bayan wani saɓani da suka samu.
Kakakin Rundunar Ƴan sandan Katsina Gambo Isah ya ce bayan wani rashin fahimta tsakaninsu, Najib ya garzaya zuwa madafi inda ya kinkimi taɓarya ya kuma fara bugawa kishiyar mahaifiyarsa Asiya Mohammed mai shekara 60 har rai ya yi halinsa.
Wanda ake zargi Najib ya kuma yi amfani da taɓaryar wajen bugawa mahaifinsa abin da ya sa ya samu karaya.
Ƴan sanda sun ce sun ƙwace taɓaryar ana kuma ci gaba da gudanar da bincike.