An dauko hoton wuri mafi nisa a sararin samaniya

An wallafa

An fitar da hoton farko da sabuwar na’urar hangen sararin samaniya ta James Webb Space Telescope ta dauko.

Hoton shi ne mafi nisa da aka taba daukowa a tarihin dan’adam.

Ya kuma kunshi hotuna ne na taurarin da nisan su ya kai na miliyoyin shekaru daga duniyarmu.

An fara nuna hoton ne ga shugaban Amurka Joe Biden a fadarsa ta White House.

A lokacin da ya yi tsokaci kan hoton, Biden ya ce wannan ya nuna cewa babu abin da Amurka ba za ta iya yi ba.

Dama dai ayyukan da aka tsara na’urar hango samaniyar za ta yi sun hada da dauko hotunan taurari na farko-farko da suka wanzu a sararin subhana.

Wadanda ake tunanin sun fara wanzuwa ne tun shekaru sama da biliyan 13 da rabi da suka gabata.

Abu na biyu kuma shi ne bincike domin gano ko akwai wasu duniyoyi a sararin samaniya da wasu halittun ke rayuwa a cikin su.

Wannan hoto da na’urar ta dauko dai shi ne na farko da aka fitar tun bayan aika ta sararin samaniya a ranar 25 ga watan Disamban 2021.

Hoton dai na wasu gungu-gungun cunkoson taurari ne da suka fara wanzuwa kimanin shekaru miliyan 600 bayan gagarumar tarwatsewar da ta haifar da taurari da duniyoyi.

Masana dai na hasashen cewa sararin samaniya da abin da ya kunsa, kamar taurari, da duniyoyi, da sauran su, sun faru ne shekaru biliyan 13.8 da suka gabata.

Ita kuma wannan na’urar hangen sararin sama an kirkire ta ne domin hango yadda samaniya ta kasance shekaru biliyan 13.5 da suka gabata.

Ta yaya na’urar hangen sararin samaniya za ta hango abubuwan da suka faru a biliyoyin shekaru da suka gabata?

Hasken rana yana isowa duniyarmu ne bayan minti takwas da tasowarsa daga rana.

Saboda haka a lokacin da muke ganin rana, shi ne yadda ta kasance a mintuna takwas da suka wuce.

Ta yin la’akari da bayanin da ya gabata – akwai taurari a sararin samaniya wadanda haskensu ke daukar shekaru kafin ya iso duniyarmu (Saboda nisa).

Saboda haka wasu taurarin da muke hangowa a yanzu, shi ne yadda suka kasance a daruruwan shekaru a baya (Ba ainihin yadda suke a yanzu ba, a inda suke).

Haske daga taurarin da suka faru jim kadan bayan gagarumar tarwatsewar da ake kira Big Bang, ya faro tafiyarsa ne (zuwa duniyarmu) tun biliyoyin shekaru da suka gabata.

Saboda haka wannan sabuwar na’urar hangen sararin samaniya za ta hango taurarin ne a yadda suka kasance tun wadancan biliyoyin shekaru, kusan daidai lokacin da suka fara wanzuwa a sararin sama.