Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masana sun gano lokaci na farko da taurari ke fara haske
- Marubuci, Daga Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC na kimiya
- An wallafa
Masana ilimin taurari sun gano lokacin da taurari suka fara haskawa.
Sun ce wannan lokacin da ake kira "wayewar gari," ya faru ne tsakanin shekaru miliyan 250 zuwa 350 bayan tunanin tushen duniya ta hanyar fashewa da ake kira Big Bang.
Sakamakon ya nuna cewa taurarin farko za su yi hasken da na'urar hangen nesa ta hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka Nasa za ta iya gani, wanda ake shirin ƙaddamarwa a wannan shekarar.
An wallafa binciken a mujallar masana ilimin taurari ta wata-wata.
Gano lokacin da taurari ke fara haske bincike ne da Farfesa Richard Ellis, na Jami'ar London a Birtaniya ya shafe rayuwarsa yana yi.
Ya shaida wa BBC cewa: "Yanzu haka an samu hujjoji da ke tabbatar da lokacin da taurari ke fara haske duniya."
Tawagar ta yi nazari kan manyan taurari shida. Suna da nisa sosai da na'urar hangen nesa mafi girma a duniya ba za ta iya tsinkaya ba sosai a kwamfuta.
Kuma sun kasance na farko da suka fara haskakawa a duniya, don haka daga lokacin da aka ɗauki hotunansu da na'urar hangen nesa a duniya, ba a daɗe da ganinsu ba bayan tunanin tushen duniya ta hanyar fashewa da ake kira Big Bang.
Ta hanyar nazarin shekarunsu, tawagar ta ƙiyasta lokacin da suke fara haske - lokacin da tauraruwar farko ta fara fita.
Dr Nicolas Laporte ne na cibiyar ilimin taurari a Cambridge ya jagoranci binciken.
Dr Laporte ya ce samun sakamakon kamar buri ne ya cika.
"Yana da kyau a yi tunanin cewa wanzuwar haske ya kasance yana tafiya cikin sararin samaniya sama da shekaru biliyan 13 sannan ya shiga cikin na'urar hangen nesa.
Abu mai ban mamaki game da kasancewa masanin taurari shi ne ikon yin tafiye-tafiye na lokaci da kuma ganin abubuwan da suka gabata," in ji shi.
Duniya ta samu shekaru biliyan 13.8 da suka gabata ta hanyar abin fashewa da ake kira Big Bang.
Bayan samun walƙiya ta farko, har zuwa lokacin zamanin duhu.
A cewar sabon binciken da aka gudanar, shekaru miliyan 250 zuwa 350 bayan babbar fashewar Big Bang, taurari na farko suka fara fitowa, suna haskaka sararin samaniya.
Kuma sabon binciken ya kuma nuna cewa gungun taurarin farko suna da haske sosai kuma za a iya ganinsu ta hanyar na'urar hangen nesa ta James Webb.
Masana ilimin taurari za su iya tabbatar da wannan muhimmin lokacin na sauyin duniya kai tsaye.
Masaniyar ilimin taurari ta Scotland, Farfesa Catherine Heymans ta ce ta yi farin ciki da wannan ci gaban.
Ta shaida wa BBC cewa: "wannan a matsayinmu na ƴan Adam wani ƙaramin ci gaba ne a duniyarmu.
"Za mu iya samar da na'urar hangen nesa da za mu iya aikawa zuwa sararin samaniya mu yi binciken duniyar kamar yadda ya kasance ɗaruruwan shekaru bayan samuwar duniya ta hanyar babbar fashewar Big Bang."
Yawancin taurarin farko sun bambanta da rana da muke gani. Amma sun haifar da wasu taurarin da aka halitta a shekaru da dama.
Masu binciken sun gano hasken taurari ta hanyar amfani da na'urorin zamani na binciken sararin samanin wato Hubble da Spitzer Space Telescope.
Sun ƙimanta shekarun taurarin ta hanyar yin nazarin yawan ƙwayoyin halittarsu a yanayinsu na taurarin. Tsofaffin taurari, sun fi girman adadin ƙwayoyin sinadarin hydrogen.
Tawagar masanan ta ƙiyasta girman nisan da taurarin. Saboda haske daga taurarin yana ɗaukar lokaci kafin mutane su gani a duniya, girman yadda suke nesa, haka kuma masana taurari ke nazarinsu.
Saboda taurari shida da aka yi nazari akansu su ne adadin da na'ura za su iya hange, kuma suna cikin na farko da aka gani.
Tawagar na buƙatar awa 70 na lokacin lura da su, ta hanyar amfani da manyan na'urori na ƙasa domin ƙiyasta nisa.
Sun haɗa da babbar na'urar Alma da VLT da Gemini South Telescope - dukkaninsu a Chile da kuma twin Keck a Hawaii.
Wannan ma'aunan sun ba tawagar masanar damar tabbatar da cewa suna lura da taurarin ne lokacin da duniya ke da shekara miliyan 550.
Sanin shekarun taurarin da kuma lokacin da suka wanzu ya ba masanan damar yin lissafin lokacin da aka haifi taurarin farko.
An kuma aiwatar da wannan ƙiyasin ta hanyar amfani da tauraro ɗaya, amma wannan ne na farko mafi ma'ana ta la'akari da rukuninsu.
Za ku iya bibiyar Pallab a Twitter.