Abubuwan da suka kamata budurwa ta sani kafin aure

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Aure wata muhimmiyar tafiya ce da ke kawo sabuwar rayuwa ga mace da namiji.

Duk da cewa mutane da yawa suna ɗaukar aure a matsayin ranar biki da shagulgula kawai, masana suna cewa aure ya fi hakan girma saboda yana buƙatar haƙuri, fahimta, sadaukarwa da kuma ilimi.

Ga budurwa, shiga gidan aure kan zo da sabuwar rayuwa mai cike da sauye-sauye, daga yadda take tafiyar da lokacinta zuwa yadda take hulɗa da mijinta da iyalansa da ma komai.

A yau, ana samun matsalolin aure da dama da suka haɗa da rashin fahimtar juna, matsin tattalin arziki, tsoma bakin wasu da kuma rashin shiri kafin shiga zaman aure.

Don gano abubuwan da kowace budurwa ya kamata ta sani kafin aure ne ya saka BBC ta tattauna da mai ba da shawara kan zamantakewar aure da kuma wata tsohuwa mai shekaru da dama a rayuwar aure.

A cewarsu, akwai muhimman abubuwa da ya kamata budurwa ta fahimta game da kanta, mutumin da za ta aura da kuma nauyin zaman aure kafin ta yanke wannan muhimmiyar shawara.

Ga wasu daga cikin abubuwan da suka ce kowace budurwa ta kamata ta sani kafin aure.

Ki san kanki

Ƙwararriyar mai ba da shawara, Sadiya Suleiman, ta ce yana da muhimmanci budurwa ta fara sanin kanta kafin aure, ciki har da burinta, irin rayuwar da take so, abubuwan da ba za ta iya jurewa ba, da yadda take magance fushi da saɓani da dai sauransu.

Ta ce "sanin kai yana taimaka wa mace wajen bayyana buƙatunta da fahimtar irin mutumin da ya dace da ita, maimakon ta shiga aure tana tsammanin mijinta ne kaɗai zai samar mata da cikakkiyar farin ciki."

Kada ki yi aure da tunanin za ki canja mutum

Wasu lokuta budurwa kan lura da wasu halaye da ba ta so a wurin wanda za ta aura, amma ta yi tunanin cewa zai canja bayan aure.

Sai dai ƙwararriyar mai ba da shawarar ta ce ya kamata budurwa ta duba halayen mutum na yanzu, domin aure shi kaɗai ba ya canja mutum.

Ta ce "yana da muhimmanci mace ta lura da yadda yake mu'amala da iyayensa da sauran mutane, da yadda yake nuna fushi da magance saɓani."

Budurwa ta tattauna muhimman batutuwa kafin aure

Sadiya Suleiman ta ce yana da muhimmanci budurwa ta tattauna muhimman batutuwa kafin aure, kamar kuɗi, aikin mace, haihuwa da tarbiyyar yara, wurin zama, hulɗa da iyalai da raba nauyin gida.

Ta ce "tattauna waɗannan batutuwa tun kafin aure na taimakawa wajen fahimtar ra'ayin juna da kauce wa saɓani a nan gaba."

Soyayya ba ta hana saɓani

Ƙwararriyar ta ce saɓani wani ɓangare ne na zamantakewa, don haka muhimmin abu shi ne yadda ma'aurata ke magance shi.

Ta ce "budurwa ta lura da yadda wanda za ta aura yake nuna hali idan ya fusata, ko yana da kunnen sauraro da kuma ba da haƙuri, ko kuma yana zagi ko barazana da tsoratarwa.

A cewarta, mutunta juna da tattaunawa cikin natsuwa na daga cikin ginshiƙan zaman aure mai kyau.

Tattauna harkokin kuɗi

Ma ba da shawarar ta ce kuɗi na daga cikin abubuwan da ke haifar da saɓani a aure, don haka ya kamata ma'aurata su tattauna harkokin kuɗi tun kafin aure.

Ta ce budurwa ta san yadda wanda za ta aura ke tafiyar da kuɗinsa.

"Ya kamata budurwa ta san ko shin yana da bashi ko yawan ciyo bashi? Yana yin tanadi? Yaya yake kallon aikin mace? Kuma ta yaya yake ganin ya kamata a tafiyar da kuɗin gida? da dai sauransu." in ji ta.

Ta ƙara da cewa "mace ma na buƙatar ilimin sarrafa kuɗi da tanadi domin makomarta.

Kada ki yi watsi da alamun da ke tayar da hankali

Sadiya Suleiman ta ce akwai wasu halaye da budurwa bai kamata ta yi watsi da su kafin aure ba, kamar tsananin kishi, neman sarrafa rayuwarta, ware ta daga iyali da abokai, cin mutunci, ƙarya da tashin hankali.

Ta ce "bai kamata a ɗauki irin waɗannan halaye a matsayin soyayya ba, domin suna iya zama alamun matsala a zamantakewa."

Budurwa ta san cewa aure ba ƙarshen burinta ba ne

Ƙwararriyar ta ce shiga gidan aure ba yana nufin mace ta daina neman ilimi, koyon sana'a ko cimma burinta bane.

Ta ce yana da muhimmanci ma'aurata su tattauna tun kafin aure game da burin kowannensu da yadda za su tallafa wa juna.

"Aure ya kamata ya kasance haɗin gwiwa. Ya kamata ku san inda kuke son rayuwarku ta dosa da yadda kowannenku zai taimaka wa ɗayan," in ji ta.

Mece ce shawarar dattijan da suka daɗe a gidan aure?

Bilkisu Dahiru, wata dattijuwa mai shekara 71 da ta shafe shekaru 50 tana zaman aure, ta ce aure yana buƙatar haƙuri, fahimtar juna da sadaukarwa. Ga wasu daga cikin shawarwarinta ga budurwa kafin aure:

Kada ki kwatanta aurenki da na wasu

Ta ce kowanne aure yana da nasa yanayi, don haka bai kamata mace ta auna rayuwarta da abin da take gani a wajen wasu ba.

Aure yana buƙatar haƙuri, amma haƙuri yana da iyaka

Ta ce ma'aurata suna fitowa daga gidaje da tarbiyya daban-daban, don haka suna buƙatar lokaci domin fahimtar juna.

Sai dai ta jaddada cewa haƙuri ba yana nufin jure cin zarafi ko abin da ke cutar da mutunci ba.

Koyi magana da sauraro

Dattijuwar ta ce "Ya kamata budurwa ta koyi iya magana da sauraro saboda ma'aurata ya kamata su riƙa tattauna matsaloli cikin natsuwa, tare da sauraron ra'ayin juna domin fahimtar juna."

Budurwa ta riƙe mutanen da za su ba ta shawara mai kyau

Ta ce samun iyali, abokai ko masu ba da shawara da za a iya dogaro da su na da muhimmanci, amma ba kowace matsala ce ya kamata a kai wa kowa ba.

Kada budurwa ta yi aure saboda matsin lamba

Dattijuwar ta gargaɗi mata da kada su yi aure saboda ganin takwarorinsu sun yi aure ko saboda matsin lamba daga iyali da al'umma.

"Hakan zai iya saka budurwa ta jefa kanta cikin rayuwa mai wuya da ƙunci." in ji ta

Budurwa ta gane cewa aure haɗin gwiwa ne

A cewar dattijuwar ya kamata budurwa ta fahimci cewa aure haɗin gwiwa ne tsakanin mutane biyu da ke buƙatar fahimtar juna da mutunta juna da taimakon juna wajen gina rayuwa.

Ya kamata budurwa ta san cewa nasarar aure ba nauyin mutum ɗaya ba ce, sai da gudummawar ma'auratan biyu.

Sadiya Suleiman ta ce babu wani shiri da zai sa mutum ya san duk abin da zai faru a gidan aure. Amma sanin kai, tattauna muhimman batutuwa, lura da halayen wanda za a aura da kyakkyawar fahimta da kuma neman shawara na iya taimaka wa budurwa ta shiga wannan sabon mataki na rayuwa saboda aure ba bikin yini ɗaya ba ne, rayuwa ce da ake gina ta a hankali.