Yadda gwamnatin Najeriya za ta cire tallafin wutar lantarki a 2027

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na kawo ƙarshen tallafin wutar lantarki daga shekara mai zuwa, 2027, a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen da take son aiwatarwa domin tabbatar da ɗorewar harkokin kuɗi a ɓangaren lantarki.

Ministan lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma'a.

Tegbe, ya ce gwamnati na tsara yadda za a cire abin da ya kira "abin da ake cewa a ɓangaren lantarki ba tare da kawo tangarɗa ga samar da wuta ko ƙara jefa masu amfani cikin wahala ba.

Ministan ya ce gwamnati na neman amincewar Shugaba Bola Tinubu domin biyan bashin da ake bin ɓangaren lantarki, wanda ya kai kimanin naira tiriliyan 3.3, tare da samar da tsare-tsaren kuɗi masu ɗorewa domin hana sake afkuwar irin wannan matsala ta taruwar bashi a gaba.

Ya ce : "Ina muku alƙawari cewa, idan Allah Ya kai mu shekara mai zuwa, za mu kawo ƙarshen wannan abin da ake kira tallafi a ɓangaren wutar lantarki."

Sai dai ya jaddada cewa kawo ƙarshen tallafin ba yana nufin za a yi karin kuɗin wutar lantarki nan take ba, yana mai musanta rahotannin da ke cewa gwamnatin tarayya na shirin ƙara kuɗin wuta ko mayar da duk masu amfani da lantarki zuwa tsarin layin wuta na Band A.

"Babu wata manufa ta wannan gwamnati ta ƙara kuɗin wutar lantarki fiye da yadda yake a yanzu, a halin yanzu," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "Idan wani yana gaya muku cewa muna son ƙara kuɗin wutar lantarki, to ba haka ba ne. Ku gaya wa 'yan Najeriya cewa babu irin wannan shiri a yanzu."

A cewarsa, babban abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai shi ne inganta samar da wutar lantarki, faɗaɗa damar samun wuta ga jama'a, da kuma tabbatar da cewa masu amfani suna biyan kuɗin adadin wutar da suka yi amfani da ita kawai.

"A halin yanzu, abin da muka sa a gaba ba ƙara kuɗin wuta ba ne. Muna son inganta ayyuka, tabbatar da samun wuta ga kowa da kuma tabbatar da cewa 'yan Najeriya suna biyan kuɗin abin da suka amfani da shi kawai."

Tegbe ya kuma ce gwamnati na tanadin hanyoyin rage tasirin sauye-sauyen ga iyalan da ke da ƙaramin ƙarfi na tattalin arziki, yana mai cewa za a ci gaba da kare masu amfani da lantarki masu rauni.

"Akwai 'yan Najeriya da ba za su iya biyan cikakken kuɗin lantarki ba. Waɗannan su ne masu rauni, kuma za mu kare su."

Ministan ya amince cewa tarin basussukan da ke cikin ɓangaren lantarki na daga cikin manyan matsalolin da ke hana samar da ingantacciyar wuta da jawo sababbin zuba jari.

Ya ce sauye-sauyen da ake shirin yi na da nufin dakatar da ci gaba da tara basussuka tare da kafa kasuwar lantarki bisa tsarin kuɗi mai ɗorewa.

Duk da shirin cire tallafin, Tegbe ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa hakan ba zai zo ne a kan ingancin samar da wutar lantarki ba.

"Ba za mu hana 'yan Najeriya samun wani abu ba. Za mu tabbatar da cewa masu amfani da lantarki suna ci gaba da samun wuta tare da ingantattun ayyukan samar da ita," in ji ministan.