Dalilai 4 da suka sa aka gaza magance matsalar tsaro a wasu jihohin Arewa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A baya-bayan nan sace wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati a arewa maso yammancin Najeriya ya sake nuna yadda wutar matsalar tsaro a yankin ke ci gaba da ci duk da yunƙurin da aka sha yi na kashe ta.

A farkon mako aka sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara, sannan kimanin awa 24 bayan haka aka sace alƙalin babbar kotu a jihar Kebbi.

Wani rahoto na kamfanin da ke nazari kan harkar tsaro a yankin Sahel na Afirka, Beacon Security and Intelligence Limited, ya yi gargaɗi tare da nuna ƙaruwar matsalolin tsaro a Najeriya musamman a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi.

Rahoton ya nuna cewa matsalar ta fi muni sosai a jihar Sokoto.

Sannan ya ce akwai buƙatar gwamnonin waɗannan jihohi da ke yankin arewa maso yamma su tashi tsaye wajen hadin-kai da aiki da gwamnatin Tarayya indai har suna son ganin matsalar tsaron ta yi sauki.

Shugaban kamfanin, Dakta Kabiru Adamu ya ce sun jima suna bayar da shawarwari, waɗanda ya ce da an yi amfani da su, da an ga sauƙin wasu abubuwan da ke faruwa na tsaro a wadannan jihohi.

''Shawara ce ga gwamnoni uku na arewa maso yammacin Najeriya na jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara, inda muke ganin ƴanbindiga a baya-bayan nan sun ƙara ƙaimi wajen hare-haren kuma suna satar jama'a don karbar kudin fansa.''

Dakta Adamu ya ƙara da cewa, ''Muna sane da cewa a baya-bayan nan akwai alƙali da kuma shugaban ƙaramar hukuma waɗanda aka sace kuma har yanzu suna hannun waɗannan ƴanbindiga da kuma irin hare-haren da ake kaiwa ƙauyuka kusan kullum.''

Dangane da abubuwan da binciken kamfanin ya nuna suna ƙra ta'azzara matsalar tsaron ya yi bayanin cewa;

''To na farko dai alƙaluma da muke ajiyewa sun nuna mana cewa a farkon rabin shekaran nan daga watan ɗaya zuwa watan shida ba jihar da matsalar tsaro ta shafa fiye da jihar Sokoto. Wannan kuma ya fito a zahiri yana nuna yadda tabarbarewar tsaron take.''

Ya ƙara da cewa,'' Ba shakka jihar Zamfara da ita kanta jihar Kebbi suna da matsaloli iri daban-daban amma kuma dangane da alkaluma abin ya fi shafar jihar Sokoto.''

Rahoton na kamfanin Beacon ya nuna cewa abubuwa ne da dama ke janyo ƙaruwar matsalar ta tsaro a waɗanann jihohi, kamar yadda shugaban kamfanin ya ƙara bayani.

  • Rashin haɗin kai:

Sau da dama masana tsaro sun sha nanata cewa haɗin kai tsakanin waɗannan jihohi a ƙoƙarin magance matsalar zai taka rawa sosai, kasancewar ƴan fashin na zirga-zirga ne tsakanin jihohi.

A tattaunawarsa da BBC, Kabiru Adamu ya ce "Abin da ke da ban mamaki shi ne yadda babu wata alaƙa mai ƙarfi tsakanin gwamnonin nan.''

Sau da yawa ko da wata jiha ta ɗauki matakin da ya haifar da samun sauƙi kan matsalar, rashin ɗaukar irin wannan mataki a jihar da ke da maƙwaftaka da ita na bai wa ƴan fashin damar tsallakawa su aikata ta'asa.

Rahoton ya ce, kusan kowane gwamna yana yin gaban kansa ne, kasancewar har yanzu babu wani tsari na bai ɗaya da suke tafiya a kai kan magance matsalar ta tsaro.

  • Rashin mayar da hankali

A lokuta da dama an sha zargin hukumomi da mayar da hankali kan yaƙi da matsalar, kasancewa ana ganin ƴan bindigar suna zirga-zirgar su a cikin daji ba tare da wani tarnaƙi ba.

Adamu ya ce ''ƴanbindigan nan suna da dama ta walwala har dai a kan babura, daga wuri zuwa wuri, babu mataki guda ɗaya tilo wanda aka ɗauka na mamaye dazukan, a hana ƴanbindigan walwala".

Ana ƙiyasin cewa akwai ƙungiyoyin ƴan bindiga da dama a dazukan da suka tashi daga arewa maso yammacin ƙasar zuwa kudu maso yammaci, cikin irin wadannan ƙungiyoyi har da masu alaƙa da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Ko a watan Disamban 2025 Amurka ta kai hari a jihar Sokoto, inda ta yi ikirarin cewa ta kai ne kan mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar IS.

Shugaban kamfanin mai nazarin harkokin na tsaro ya ce ba wai gwamnonin jihohin ba sa wani abu ba ne: ''Kwarai suna yin abubuwa da yawa kamar a baya-bayan nan jihar Sokoto ta sayi motoci har ma da masu sulke ta ba bangarori na tsaro.''

''To amma inda matsalar take a fahimtarmu har yanzu in aka je kauyuka za a ga babu matakai na dindindin na tsaro ga jama'a.''

  • Iyaka da ƙasashen ƙetare

Najeriya na iyaka mai tsawo da Jamhuriyar Nijar wadda ta kai tsawon kilomita 1,497, kuma jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara duk suna daga cikin wadanda ke kan wannan iyaka.

Kabiru Adamu ya ce wata matsalar da ke yin tarnaƙi ga samar da tsaron shi ne: "jihohin nan duka suna da iyaka da kasashen waje har dai ma kasar Nijar".

Sau da dama hukumomi sun sha sanar da kamawa ko kashe masu aikata laifuka waɗanda ke zirga-zirga tsakanin Najeriyar da Jamhuriyar Nijar, musamman ma masu safarar makamai.

Ƙarin wasau daga cikin matsalolin da rahoton ya bayyana kuma sun hada da, rashin saka al'ummomin yankin da matsalar ta shafa a cikin tafiyar.

Me ya kamata a yi?

Dangane da abin ya kamata a yi a jihohin, Dakta Adamu ya ce, sun dade suna ba gwamnonin jihohin shawara kan abubuwan da ya kamata su yi amma ba a yi.

''To amma yanzu abin ya kai lokacin da buƙatar mu fito fili mu ƙara magana saboda burin da muke da shi na ƙoƙarin taimaka wa jihohin nan''.

''Har kullum abin da muke kara jaddadawa shi ne samun hadin kai tsakanin gwamnonin nan ta yadda jama'a waɗanda ake mulka za su ga tasirin abin da suke yi musamman a kan harkar tsaro,'' in ji shi.