Sojojin Najeriya sun kama mutum shida kan zargin taimakawa ISWAP a Borno
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun kama mutum shida da ake zargi da taimaka wa mayaƙan ISWAP wajen gudanar da ayyukansu a Damasak da ke Jihar Borno.
A cewar rundunar, an kama mutanen ne a ranar 27 ga Yulin 2026 bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewa suna taimaka wa ƙungiyar wajen samar da kuɗaɗe ta hanyar saye da sayar da shanu a kasuwannin Gubio, Damasak da Ajuwango.
Sojojin sun ce sun ƙwace makamai da mota da kuma kuɗi Naira 317,950 daga hannun waɗanda ake zargin.
Rundunar ta bayyana cewa waɗanda aka kama na ci gaba da fuskantar bincike, tana mai jaddada aniyarta ta ci gaba da lalata hanyoyin samar da kuɗi da kayan aiki ga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.