'Cunkoson ɗalibai a firamaren da na koyar ya sa babu inda zan tsaya a ajin'

Ɗaliban firamare

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wannan labari yana cikin jerin labaran da BBC Hausa za ta gabatar bayan neman jin ra'ayoyin ƴan Najeriya a manyan fannonin da suka fi shafi rayuwarsu.

Shiri ne na musamman da BBC ta tsara dangane da shirye-shiryen babban zaɓen ƙasar za a gudanar daga watan Fabrairun 2023.

Fannonin da za a yi duba a kai su ne na tsaro da ilimi da tattalin arziki da lafiya da kuma cin hanci.

Daruruwan mutane ne suka aiko da labaransu, kuma za mu wallafa 25 ne kawai, ɗaya a kowace rana daga 10 ga Oktoban 2022.

Matsalolin da 'yan Najeriya ke ciki game da harkokin ilimi na da yawan gaske; kama daga yajin aiki, da ƙarancin kayan aikin, da ƙarancin malaman kansu.

Sai kuma uwa uba cunkoson ɗalibai a manya da kuma makarantun firamare da sakandare.

Wani ma'abocin BBC Hausa ya ba mu labarin yadda ya dinga koyar da yara 200 zuwa 300 cikin aji ɗaya a wata firamare da ke Jihar Kano.

'Babu inda malami zai saka ƙafarsa ma a wani ajin'

"Akwai lokacin da na taɓa riƙe wani aji, tsakanin aji da aji ne aka katange, ba ma cikakken aji ba ne, amma wallahi na ɗauki yara sama da 200," a cewar Nura Mustapha mazaunin unguwar Rimin Kebe.

Nura ya koyar a makarantar Rimin Kebe Special Primary School da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo a Jihar Kano daga shekarar 2009 zuwa 2011.

Ya yi aiki ne a matsayin malamin sa-kai cikin wani shirin taimako da ƙungiyarsu ta ɗalibai ke gudanarwa mai suna Rimin Kebe Students Association (RISA).

Matashin mai shekara 37 ya fara koyar da 'yan aji 1 ne, waɗanda ba su san komai ba a rayuwarsu.

"Aji 1 ne, yaran ba abin da suka sani. Ni nake koya musu kusan komai, har Arabiyya, na yi musu jarrabawa, na shigar a takardar rahoto kuma na fitar duka ni kaɗai.

"A wannan unguwa ta Rimin kebe firamare ɗaya gare mu, amma ta yi wa al'umar wannan unguwa kaɗan saboda yawan jama'a."

Nura ya ƙara da cewa a kowane aji cikakke ba a rasa yara 300 zuwa 400.

"Wallahi ba na samun damar yin abin da nake so yadda ya kamata saboda a kowane aji cikakke ba a rasa yara 300 zuwa 400."

Wata matsala da Nura ya sake bayyanawa ita ce ta ruwan sama, wanda a duk lokacin da aka yi shi sai makarantar "ta cika da ruwa makil kai ka ce wani rafi ne".

"Wallahi abin yana damu na, saboda wani lokacin ba za ka iya koyarwar yadda ya kamata ba. Inda za ka saka ƙafafuwanka ma ka yi rubutu a jikin allo aiki yake zama."

Game da ko ana samun yaran da ke fahimtar karatun, ya ce: "Akan samu waɗanda ke fahimta ɗin amma da yawa ba sa ganewa saboda cunkoson ajin."

Kiran da Nura ya yi: "Daga ƙarshe ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su duba wannan damuwa tamu a wannan unguwa mai dauke da jama'a masu tarin yawa domin kawo mata agaji wajen gina sababbin azuzuwa ko kuma kafa wasu makarantun."