Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland na kafa tarihin cin kwallaye duk da kakar farko a Premier
Ranar Asabar Manchester City ta doke Southampton da ci 4-0 a gasar Premier da suka kara a Etihad.
Tun kan hutu City ta ci kwallo biyu ta hannun Joao Cancelo da Phil Poden, bayan da suka koma zagaye na biyu Riyad Mahred da Haalamd suka kara cin kwallaye.
Kwallo na 15 kenan tsohon dan wasan Borussia Dortmund ya ci a babbar gasar tamaula ta Ingila a bana.
Kenan Haaland ya zura 20 a raga a dukkan wasa 13 da ya yi wa kungiyar Etihad, wadda ta dauko shi a kakar nan daga Jamus.
Hakan na nufin ya kan ci kwallo daya a duk wasa kenan a Premier League.
Ya zama na biyu a City, bayan Sergio Aguero a kakar 2019, wanda ya ci kwallo a wasa bakwai a jere a gasar Premier League da ya yi.
Dan wasan da ta dauka kan fam miliyan 51 daga Borussia Dortmund ya ci kwallo iri daya da yawan wadanda Kevin de Bruyne ya zura a raga a kakar 2021/22 da City ta lashe Premier League.
Kafin fara kakar nan Micky Quinn shi ne kan gaba a cin kwallaye a wasa tara da fara babbar gasar tamaula ta Ingila a tarihi mai 11 a raga a lokacin.
Sai dai dan wasan da ya ci kwallo da wuri da fara kakar Premier League shi ne Andy Cole mai 15 jumulla.
Kungiyoyin da Haaland ya ci a Premier ta kakar 2022/23.
Premier League Lahadi 7 ga watan Agusta
- West Ham 0 - 2 Man City
Ya ci kwallo biyu
Premier League Asabar 13 ga watan Agusta
- Man City 4 - 0 Bournemouth
Bai ci kwallo ko daya ba
Premier League Lahadi 21 ga watan Agusta
- Newcastle 3 - 3 Man City
Ya ci kwallo daya
Premier League Asabar 27 ga watan Agusta
- Man City 4 - 2 Crystal Palace
Ya ci kwallo uku
Premier League Laraba 31 ga watan Agusta
- Man City 6 - 0 Nottm Forest
Ya ci kwallo uku
Premier League Asabar 3 ga watan Satumba
- Aston Villa 1 - 1 Man City
Ya ci kwallo daya
Premier League Asabar 17 ga watan Satumba
- Wolves 0 - 3 Man City
Ya ci kwallo daya
Premier League Lahadi 2 ga watan Oktoba
- Man City 6 - 3 Man Utd
Ya ci kwallo uku
Premier League Asabar 8 ga watan Oktoba
- Man City 4 - 0 Southampton
Ya ci kwallo daya
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier a bana:
- Erling Haaland Manchester City 15
- Harry Kane Tottenham 8
- Phil Foden Manchester City 6
- Roberto Firmino Liverpool 6
- Aleksandar Mitrovic Fulham 6
- Ivan Toney Brentford 6
- Leandro Trossard Brighton 5
- Gabriel Jesus Arsenal 5
- James Maddison Leicester City 5
- Gabriel Martinelli Arsenal 4
- Wilfried Zaha Crystal Palace 4
- Miguel Almiron Newcastle United 4
- Rodrigo Leeds United 4
- Alexis Mac Allister Brighton 4