Abin da ya kamata ku sani kan zaɓen gwamna a Kogi da Imo da Bayelsa

Asalin hoton, INEC
A yau ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ke gudanar da zaɓukan gwamna a jihohin Kogi da ke tsakiyar Najeriya, da Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar, sai jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Hukumar INEC ta tabbatar wa BBC cewa zaɓen da ake gudanarwa yau a jihohin na gwamna ne kawai.
Jihohin uku na daga cikin jihohin ƙasar bakwai da ba a gudanar da zaɓen gwamna ba a lokacin babban zaɓen ƙasar na watan Maris ɗin 2023.
Cikin wani saƙo da hukumar zaɓen ta fitar a shafinta na X, ta ce kimanin mutum miliyan biyar ne da suka karɓi katunan zaɓensu ake sa ran za su fito domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na yau, cikin jihohin uku.
INEC ta ce wannan shi ne karo na farko a tarihinta da take gudanar da waɗanan zaɓuka a rana guda cikin jihohin uku da ke yankunan ƙasar daban-daban.
Tun a ranar Alhamis da Juma'a ne hukumar ta rarraba kayayyakin zaɓen zuwa sassa daban-daban na jihohin.
Haka nan mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar wa mazauna jihohin samar da tsaro a lokacin zaɓukan.
Ya kuma gargaɗi ƴan siyasa da su guji tayar da hargitsi a jihar, inda ya yi kira ga jam'in tsaro da su tabbatar tsaron lafiyar mazauna jihar a lokacin gudanar da zaɓukan.
A nata ɓangare hukumar ƴan sandan ƙasar ta ce ta tanadi isassun jami'an tsaron da za su taimaka wajen gudanar da zaɓukan cikin lumana, ba tare da hargitsi ba.
Jihar Kogi

Asalin hoton, TWITTER/FACEBOOK
Ƴan takara 18 ne ke fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Kogi, sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin ƴan takarar manyan jam'iyyun APC, Ododo Ahmed Usman da Sanata Dimo Melaye na PDP, sai Murtala Yakubu Ajaka na jam'iyyar SDP.
Mutum 1,932, 654 ne suka yi rajistar zaɓe a jihar Kogi, yayin da mutum 1,833,160 suka karɓi katin zaɓensu kamar yadda bayanan hukumar INEC ɗin suka nuna.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa manyan ƴan takarar uku da ke sahun gaba a zaɓen sun fito ne daga ƙabilu daban-daban, kamar Ebira, Igala, da kuma Okun, kuma hakan zai iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaɓen.
Sun ƙara da cewa yayin da jam'iyyar APC za ta iya samun yawan ƙuri'u daga tsakiyar jihar, SDP za ta iya bayar da mamaki a gabashin jihar, inda ita kuma PDP mai ɗimbin magoya baya a yammacin jihar, za su zaɓi Dino Melaye.
Sauran ƴan takarar su ne:
- Jibrin Usman Oyibe – A
- Braimoh Olayinka Adenehon – AA
- Achimugu Augustine Abu – AAC
- Abejide Leke Joseph – ADC
- Elukpo Julius – ADP
- Ilonah Idoko Kingsley – APGA
- Isah Dauda Utenwojo – APM
- Onaji Sunday Frank – APP
- Muhammad Kabir Umar – BP
- Okeme Adejoh – LP
- Musa Saliu Mubarak – NNPP
- Dirisu Bala Abdulghafar – NRM
- Dr. Abdullahi Bayawo – PRP
- Omale Samson Agada – YPP
- Suleiman Taiye Fatima - ZLP
Jihar Imo

Asalin hoton, HOPE UZODINMA/FACEBOOK
Hukumar zaɓen ƙasar ta ce mutum 2,419, 922 ne suka yi rajistar zaɓe a jihar, yayin da mutum 2,318,919 suka karɓi katunan zaɓensu.
Manyan ƴan takarar da ke kan gaba a zaɓen gwamnan jihar, sun haɗa da gwamnan jihar, Hope Uzodinma na jam'iyyar APC. wanda ke neman wa'adin mulki na biyu.
Mista Uzodinma - wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne - na neman wa'adin mulkin jihar karo na biyu.
Sai Athan Achonu na jam'iyyar LP, wadda ke da farin jini a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Samuel Anyanwu na jam'iyyar PDP da kuma Tony Ejiogu na jam'iyyar APGA, da Ben Uche Odunze na NNPP, sai kuma Obinna Bright Ekwelem na jam'iyyar SDP.

Asalin hoton, INEC
Jihar Bayelsa
Hukumar INEC ta ce kimanin mutum 1,056,862 ne suka yi rajistar zaɓe jihar, inda mutum 1,017,613 suka.
Ƴan takara 16 ne ke fafatawa a zaɓen domin neman ɗarewa kujerar gwamnan, ciki har gwamnan jihar, Sanata Douye Diri na jam'iyyar PDP da ke neman wa'adin mulki na biyu.
Daga cikin manyan ƴan takarar da ke fafatawa a zaɓen na yau har da tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva na jam'iyyar APC, da Udengs Eradiri na LP.













