Barcelona ta ci gaba da zama ta uku a teburin La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta je ta doke Sevilla 4-1 a wasan mako na 23 a La Liga da suka kara ranar Lahadi - kenan ta ci gaba da zama ta uku a kan teburi.
Robert Lewandowski ne ya fara cin ƙwallo a minti na bakwai da take leda, sai dai mai masaukin baƙi ta farke minti ɗaya tsakani ta hannun Ruben Vergas.
Daga baya ne Barcelona ta kara na biyu ta hannun Fermin Lopez, sannan Raphinha ya ci na uku.
Daf da za a tashi daga wasan ne Barcelona ta ci na huɗu ta hannun Eric García, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take bukata a karawar.
Sai dai Barcelona ta karasa fafatawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Fermin Lopez jan kati a minti na 62.
Wannan shi ne wasa na biyu da suka buga a bana a gasar, bayan da Barcelona ta doke Sevilla 5-1 ranar 20 ga watan Oktoban 2024.
Waɗanda suka ci wa Barcelona ƙwallayen sun haɗa da Robert Lewandowski da Pablo Torre da kowanne ya ci biyu da kuma Pedri da ya zura ɗaya a raga.
Ita kuwa Sevilla ta zare ɗaya ta hannun Stanis Idumbo Muzambo saura minti uku a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 48, bayan kammala wasannin mako na 23 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Real Madrid wadda ta tashi 1-1 da Atletico Madrid ranar Asabar tana matakin farko da maki 50 da tazarar maki ɗaya tsakani da Atletico ta biyu.
Barcelona wadda ta kai zagaye na biyu a Champions League kai tsaye, ba ta da wani wasa nan kusa sai ranar Litinin 17 ga watan Fabrairu da za ta karɓi bakuncin Rayo Vallecano.
Tuni dai Barcelona wadda ta lashe Spanish Super Cup a bana a Saudi Arabia ta kai daf da karshe a Copa del Rey, sakamakon da ta doke Valencia 5-0 ranar Alhamis.












