Brazil za ta kara da Croatia a Quarter finals bayan cin Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Brazil ta doke Koriya ta Kudu da ci 4-1 a wasan zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya da suka kara a Qatar ranar Litinin.
Brazil ta ci kwallayenta hudu tun kan hutu ta hannun Vinicius Junior, sannan Neymar ya kara na biyu a bugun fenariti.
Brazil ta ci na uku ta hannun Richarlison da kuma ta hudu ta hannun Lucas Paqueta.
An je hutu Brazil ta gama cin hudu, kuma bayan da aka koma zagaye na biyu ne Koriya ta zare daya ta hannun Paik Seun.
Ranar Juma'a Brazil za ta kara da Croatia a wasan daf da karshe a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.
Croatia ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan cin Japan 3-1 a bugun fenariti.
Tun farko sun tashi 1-1 aka kuma yi karin lokaci zuwa minti 120 amma ba ci, hakan ya sa aka yi bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda Croaria ta kai bantenta.
Brazil mai kofin duniya biyar ta ci karawa ta 76 a Gasar Kofin duniya, wadda rabonta da kofin tun 2002.
Wannan shi ne wasa na takwas da aka kara tsakanin Brazil da Koriya ta Kudu, inda Brazil ta yi nasara a bakwai, Koriya ta ci daya.











