Arsenal da Man United na gogayya kan Sane, Liverpool za ta sabunta kwantiragin Salah

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United da Arsenal na son ɗauko tsohon ɗan wasan Manchester City Leroy Sane daga Bayern Munich, kwantiragin ɗan wasan mai shekara 28 zai kare a ƙungiyar da ya ke taka wa leda a kaka mai zuwa. (Bild - in German, subscription required)

Liverpool na ci gaba da tattaunawa kan ɗauko ɗan wasan gaba na Masar Mohamed Salah mai shekara 32, kan sabunta kwantiraginsa. (Florian Plettenberg)

Arsenal na sa ido kan ɗan wasan Real Sociedad da kuma na Sifaniya Martin Zubimendi, domin ganin ta ɗauko ɗan wasan mai shekara 25. (Independent)

Barcelona da Real Madrid na son ɗan wasan baya na Nottingham Forest, ɗan asalin Brazil Murillo, mai shekara 22. (Sport in Spanish).

Manchester United na son ɗan wasan Bournemouth, Milos Kerkez. (Football Transfers)

Liverpool dai na son dan wasan PSV Eindhoven Ricardo Pepi, daidai lokacin da tauraron dan wasan mai shekara 21ke haskawa, sakamakon son shi da kungiyoyin Bayern Munich, da Borussia Dortmund da Atletico Madrid ke yi. (Caughtoffside)

Manchester United na duba yiwuwar sauya dan wasa Dinamo Zagreb da maye gurbinsa da dan wasan tsakiya na Croatia Martin Baturina, mai shekara 21, idan aka bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Junairu, duk da cewa kungiyoyin Barcelona da Atletico suma na son dan wasan. (Teamtalk)

West Ham na son dan wasan Botafogo kuma na gaba a Brazil Igor Jesus, 23, domin karfafa 'yan wasansu masu kai hari a filin tamaula. (Football Insider)

Shugaban kungiyar Newcastle United ya nutsu bai daga hankali ba kan kwantiragin mai kai hari na Sweden wato Alexander Isak, duk da cewa har yanzu dan wasan bai zauna da kyau a kulub din ba. (Newcastle Chronicle)