Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle na farautar Sane, Ƙungiyoyi na rububin Ricci
Newcastle na farautar ɗan wasan Bayern Munich mai shekara 28 daga Jamus, Leroy Sane, wanda kwantiraginsa ke karewa a karshen kaka. (Football Insider)
Bayern Munich ta matsa kaimi a tattaunawa da Jamal Musiala, mai shekara 21, kan tsawaita zamansa a Jamus, sai shekarar 2026 kwantiragin da yake kai yanzu zai cika wa'adinsa. (Sport1 - in German)
AC Milan, Inter Milan da Napoli dukkaninsu na zawarcin ɗan wasan tsakiya a Torino mai shekara 23, Samuele Ricci. (Calciomercato - in Italian)
Daraktan wasanni a Bayern Munich Max Eberl ya kare matsayarsu na sayar da ɗan wasan baya a Netherlands, Matthijs de Ligt, mai shekara 25 ga Manchester United, ya kuma shaida cewa a yanzu 'yan wasan tsakiyarta na da karfi wajen ba su kariya. (Mirror)
Hamshakin ɗan kasuwa a Amurka, John Textor na son Fitaccen mawaki Jay-Z ya shiga cikin masu gabatar da tayin sayen Everton.(Sun)
Ɗan wasan tsakiya a Jamus, Joshua Kimmich, mai shekara 29, ya shirya sabunta yarjejeniyarsa a Bayern Munich. (Sky Sports Germany)
Barcelona dai ta nuna zawarcinta kan Kimmich, ganin kwantiragin da yake kai a yanzu na gab da karewa a kungiyarsa ta Bundesliga club. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Akwai tunanin Liverpool ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Sevilla mai shekara 24, Loic Bade, duk da cewa ana alakanta shi da ƙungiyoyin Faransa. (Matteo Moretto, via Yahoo)
Ɗan wasan Jamaica Michail Antonio, mai shekara 34, da kuma na Ingila, Danny Ings, mai shekara 32, na iya barin West Ham kafin karshen wa'adinsu. (Football Insider)
Barcelona ta ce tana son cigaba da ajiye ɗan wasan gaba a Sifaniya, Ansu Fati duk da cewa ɗan wasan mai shekara 21 bai buga mata wasa a lig ba tun Agustan 2023, kafin tafiya aro Brighton. (Fabrizio Romano)
Manchester United ta fuskanci koma baya a lokacin da tayi yunkurin saye ɗan wasan Senegal mai shekara 20, Mikayil Fayekafin ya koma Rennes daga Barcelona. (Inkubator podcast, via Teamtalk)