Chelsea ta ɗauki Neto daga Wolves kan £54m

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta amince ta biya Wolverhampton Wanderers £54m, domin ɗaukar Pedro Neto.
Ɗan wasan tawagar Portugal zai je a auna koshin lafiyarsa, daga nan ya koma Stamford Bridge, inda Chelsea ta kashe sama da £200m, wajen sayen ƴan ƙwallo a bana.
Daga karshe Chelsea ta kulla yarjejeniyar sayen ɗan wasan Wolves - kan £51.3m da karin £2.6m na tsarabe-tsarabe, bayan da aka ƙi sallama tayi karo biyu da ta yi.
Tun a farkon mako Chelsea ta bukaci a kulla yarjejeniya ciki har da anbaton bayar da David Datro Fofana da Trevoh Chalobah cikin cinikin - amma ta ƙi amincewa daga nan ta yi tayin biyan kuɗi, amma Wolves ba ta yadda ba a ranar Alhamis.
Mai shekara 24 ya buga karawa 135 da cin ƙwallo 14 tun bayan da ya koma Wolverhampton daga Lazio a 2019.
Idan har cinikin ya kammala, Neto zai zama mai tsada da Wolves ta sayar, bayan Ruben Neves da ya koma Al-Hilal ta Saudi Arabia kan £47m a bara.






