De Jong ya zabi ci gaba da zama a Barcelona maimakon Man United

Frenkie de Jong

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Frenkie de Jong "na son ci gaba da taka leda" a Barcelona, duk da Manchester United na kokarin sayen dan kwallon, in ji Joan Laporta.

United ta amince da farashin fam miliyan 63.5, domin sayen dan wasan tawagar Netherlands, mai shekara 25, a watan jiya, amma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.

De Jong ya shiga wasan da Barcelona ta doke Pumas UNAM da ci 6-0 a zagaye na biyu a karawar sada zumunta ya kuma ci kwallo daya.

''Dan wasan Barcelona ne mai kwarewa, kuma muna son ya ci gaba da zama a Camp Nou,'' kamar yadda Laporta ya sanar.

''Kungiyoyi da yawa na taya dan kwallon, amma muna son ya zauna, shi kansa baya son barin Barcelona,''

Ana alakanta De Jong da cewar zai koma Chelsea, bayan da United ta dade tana son daukar dan kwallon, wanda ya taka leda karkashin Erik ten Hag a Ajax.

Ranar Lahadi United ta yi rashin nasara a Old Trafford da ci 2-1 a hannun Brighton a wasan farko da fara Premier League kakar 2022/23.

Wasu rahotanni na cewar Barcelona na bukatar De Jong ya amince a rage masa albashi, domin ya ci gaba da zama a Camp Nou, wadda ke fama da matsin tattalin arziki.

Rahoton ya kara da cewar kungiyar ta Sifaniya da dan kwallon Netherlands na takaddama kan wasu albashin dan kwallon da ya kamata a biya shi a yanzu, wadanda ya daga kafa.

Barcelona ta kashe fam miliyan 120 wajen daukar 'yan wasa a bana da suka hada da Robert Lewandowski da Raphinha da Jules Kounde da kuma Andreas Christensen da kuma Franck Kessie.