Tottenham ta ɗaukaka kara kan dakatar da Bentancur

Rodrigo Bentancur

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham ta ɗaukaka kara kan dakatar da Rodrigo Bentancur wasa bakwai da aka yi, sakamakon kalaman ɓatanci ga Son Heung-min.

Ƙungiyar da ke buga Premier League ta ce hukuncin ya yi tsauri, bayan da wani kwamiti mai zaman kansa ya samu ɗan ƙwallon da laifi.

To sai dai Tottenham ta amince da tarar da aka ci ɗan wasan £100,000, an bukaci ya je neman ilimin da za a tsara masa na wajibi a kansa.

Hukumar ƙwallon kafar Ingila ce ta tuhumi ɗan wasan tun cikin watan Satumba, saboda wasu kalaman da ya yi a lokacin wata hira a talabijin a Uruguay a watan Yuni.

Bentacur, wanda ya musanta zargin, yanzu an dakatar da shi daga buga dukkan wasannin Ingila da ake gudanarwa.

Ba zai buga Premier League ba da Manchester City da Liverpool da na Chelsea da sauransu, har da wanda ƙunguiyar za ta kara da Manchester United a kwata fainals a League.

Sai dai zai iya buga wa Tottenham gasar zakarun Turai ta Europa League da ƙungiyar ke yi.