Arsenal ta sha da kyar a hannun Bournemouth a Emirates

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal da doke Bournemouth da cin 3-2 a wasan mako na 26 a gasar Premier da suka fafata ranar Asabar a Emirates.

Minti daya da fara wasa Bournemouth ta ci kwallo ta hannun Philip Billing, sannan ta kara na biyu ta hannun Marcos Senesi a zagaye na biyu.

Daga baya ne Thomas Partey ya farke wa Arsenal daya, sannan Ben White ya ci na biyu, sai kuma Reiss Nelson ya zura na uku a raga daf da za a tashi.

Hakan ne ya bai wa Gunners maki ukun da take bukara a shirin da take na lashe babban kofin gasar tamaula ta Ingila a bana.

Da wannan sakamakon saura maki biyar tsakanin Arsenal mai jan ragama teburin bana da Manchester City ta biyu.

Arsenal tana da maki 63, ita kuwa kungiyar Etihad mai rike da kofin bara tana da maki 58.

Rabon da Arsenal ta dauki Premier League tun bayan kakar 2003/04, karkashi Arsene Wenger.

Man City ta doke Newcastle United da ci 2-0 ranar Asabar a Etihad.

Arsenal za ta ziyarci Sporting domin buga wasan farko a zangon 'yan 16 a Europa League ranar 9 ga watn Maris.

Kwana uku tsakani Gunners za ta fafata da Fulham a wasan mako na 27 a gasar Premier League a Craven Cottage.