Ba zan iya maye gurbin Rodri ba a City - Gonzalez

Asalin hoton, Getty Images
Nico Gonzalez ya ce ba zai iya maye gurbin Rodri a Manchester City ba, amma zai ci gaba da bayar da gudunmuwar da ƙungiyar za ta kai ga samun nasarori.
City ta sayo ɗan kasar Sifaniya kan £50million daga Porto a watan Janairu, domin ya maye gurbin Rodri, wanda ke jinya.
Gonzalez ya fara buga wa City tamaula a lokacin da take fuskantar kalubale a kakar nan, har da rashin Rodri, wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or.
Ranar Lahadi City mai rike da Premier League ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Liverpool a Etihad a gasar ta Premier.
Hakan ya sa ƙungiyar Anfield ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin Premier da tazarar maki 11 tsakani da Arsenal ta biyu da tazarar maki 20 tsakani da City.
City, wadda take mataki na huɗu a kan teburi tana fatan samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a baɗi, bayan da Real Madrid ta yi waje da ita a Champions League a zagayen neman shiga matakin ƴan 16.
Pep Guardiola ya kwatanta Gonzalez a madadin Rodri, saboda rawar da ya taka a lokacin da City ta doke Newcastle United 4-0 a Premier League.
To sai dai Gonzalez ya ce ''Yanzu na fara wasa a City, kuma ban saba fuskantar zakakuren ƴan ƙwallo ba kamar su Mohamed Salah da sauransu.''
''Ba a fara kakar Premier League da ni ba, amma zan ci gaba da sa ƙwazo duk da koma baya da City ke fuskanta a bana.''
City mai maki 44 a mataki na huɗu a teburin Premier ta ci wasa 13 da canjaras biyar aka doke ta karawa takwas a babbar gasar tamaula ta kakar nan.
Ranar Laraba Tottenham za ta karɓi bakuncin City a Premier, daga nan a fafata tsakanin City da Plymouth a FA Cup ranar Asabar 1 ga watan Maris ɗin 2025.












