Man City ta sanya Walker a kasuwa, Liverpool na neman mai maye gurbin Van Dijk

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na son siyar da kyaftin ɗin kulod ɗin Kyle Walker, mai shekara 34, kan farashin fam miliyan 15 a bazara mai zuwa. a halin yanzu Kulob ɗin Al-Ahli na Saudiya ke zawarcin ɗan wasan na Ingila. (Daily Star)
Liverpool ta fara zawarcin ɗan wasan bayan Borussia Dortmund dan ƙasar Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Virgil van Dijk idan ɗan ƙasar Holland ɗin ya bar ƙungiyar a bazara mai zuwa. (Caught Offside)
Manchester City da Liverpool na nuna sha'awarsu kan ɗan wasan gaban Brighton ɗan kasar Argentina Facundo Buonanotte, mai shekara 19, wanda ke zaman aro a Leicester City. (Fichajes - in Spanish)
Bournemouth za ta buƙaci "kudade masu yawa" domin sayar da ɗan wasan bayan Hungary Milos Kerkez, mai shekara 20, wanda Liverpool da Arsenal da Manchester United ke nuna sha'awa a kansa. (Football Insider)
Manchester United na iya sake dawo da ɗan wasan baya na gefen hagu Alvaro Fernandez, mai shekara 21, wanda ya koma Benfica a kan kwantiragin dindindin a bazara kuma wanda Liverpool da Real Madrid sanya wa ido. (Talk)
Arsenal ta samu ƙwarin guiwa idan har tana son ɗaukar ɗan wasan Bournemouth Antoine Semenyo, mai shekara 24, bayan ya ce shi masoyin Gunners ne kuma yana son buga gasar zakarun Turai. (Football 365)
Barcelona ta fara tattaunawa kan sabunta kwantiragin ɗan wasan bayanta Ronald Araujo, mai shekara 25 wanda Manchester United da Chelsea ke nema - da kuma ɗan wasan tsakiya Frenkie de Jong, mai shekara 27, wanda har ila yau United ke zawarcinsa. (90 min)
Akwai almaun cewa ɗan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 31, ba zai sake bugawa Juventus wasa ba idan dakatarwar da aka yi masa ta ƙare a watan Maris bayan wani darektan kulob ɗin ya ce tawagar ta kammala ba tare da shi ba. (DAZN)
Sabon kocin Ingila Thomas Tuchel zai samu alawus ɗin Fam miliyan uku idan ya kai Ingila ga nasara a gasar cin kofin duniya ta 2026. (Sun)










