Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Kano da Zamfara har aƙalla 'mutum 16' suka mutu

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumomi a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun tabbatar da wani hari da ake zargin wasu ƴan bindiga sun kai a kasuwar Sabon Gari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wani.

Shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Ibrahim Abdullahi Muhammad ne ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin inda ya ce harin ya shafi wani mai sayar da batir a kasuwar wanda ƴan bindigar suka buɗe masa wuta lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa, sai kuma wanda ya jikkata sakamakon harbi a ƙirji da cinya da hannu kuma a cewarsa, yana samun kulawa a wani asibiti da ke jihar.

A cewarsa zai yi wuya a iya tantance yawan mutanen da lamarin ya shafa saboda a lokacin da aka kai harin, mutane suna ta neman tsira "wani ma tun da bindiga ce ya ji harbi, ko da ya faɗi ya ji ciwo zai iya tashi ya gudu."

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce zuwa yanzu hankalin jama'ar yankin ya kwanta saboda gwamnati ta jibge jami'an tsaro domin sa ido.

Ya ce duk da babu cikakken bayani game da harin, rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun je ne a kan babura.

Harin Ruwan Jema a jihar Zamfara...

Ita ma gwamnatin jihar Zamfara mai fama da matsalar tsaro ta tabbatar da harin da wasu ƴan bindiga suka kai ƙauyen Ruwan Jema a ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Gwamnatin ta ce kawo yanzu babu sahihan bayanai game da adadin mutanen da suka mutu ko aka yi garkuwa da su sai dai ta sanar da aike jami'an tsaro zuwa yankin domin tantance abin da ya faru.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahotanni dai sun ce aƙalla mutum 15 ne suka mutu a harin da aka kai yankin da ya fuskanci hare-hare inda ƴan bindiga ke garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ta Zamfara, Malam Ibrahim Dosara ya faɗa wa BBC dalilan da suka sa aka gaza samun cikakken bayani kan harin bayan da aka kai shi.

Ya ce "wurin yana da wuyar zuwa musamman yanzu da damina, tituna babu kyawu, wayar sadarwa ma wahala ce samu zuwa wajen." A cewarsa, gwamnati tana bakin ƙoƙarinta na ganin ta magance abubuwan da ke janyo cikas a yunƙurinta na yaƙi da hare-haren ƴan bindiga.

Ya bayyana cewa "Gwamnati tana tsare-tsare na tabbatar da cewa an yi tituna da hanyoyin da za a kai wajen mutane, maganar da nake Sarkin garin ba ya zama a wajen saboda mawuyacin halin da ƙauyen ke ciki."

Ko a watan Yuli ma ƴan bindiga sun kai hare-hare a garin. Sama da shekaru biyu dai ƴan bindigar na barazana ga jama'a a yankunan arewacin Najeriya inda suka kama ɗaruruwan jama'a ta hanyar yin garkuwa da su da kuma saka tsoron yin balaguro a cikin rayukan jama'a.