Abin da ya kamata ku sani kan ƙwallon mata ta Afirka ta 2022

An wallafa

Ranar 2 ga watan Yuli za a fara gasar kwallon kafar mata a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco za ta karbi bakunci, wadda ake kira Women's Africa Cup of Nations (WAFCON).

Najeriya kasar da ta lashe gasar a baya, ta sanya sunan Asisat Oshoala da Ashleigh Plumptre cikin tawagarta da za ta halarci gasar.

Kocin kungiyar, Randy Waldrum, ya cire sunan 'yan wasa Gift Monday da Ngozi Okobi-Okeoghene daga tawagarsa.

Tun da fari sai da hukumar kwallon kafar kasar ta NFF ta shiga tsaka mai wuya lokacin da take son rage sunayen yan kwallon daga 32 zuwa 28 da za a halarci gasar da su.

Kawo yanzu 'yan wasan Najeriya 28 da za su wakilci Najeriya a wannan babbar gasa suna Moroko domin buga gasar.

Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da wannan gasar ta bana.

Kasar da za ta karbi bakuncin gasar

Za a fara WAFCON 2022 a ranar 2 ga watan Yuli zuwa 23 , kuma za a yi gasar a Moroko.

Tawagar Najeriya da ake kira Super Falcons za ta fafata da Bayana Bayana ta Afrika ta Kudu a ranar 4 ga watan Yuli a matakin rukunin C.

Sauran kasashe biyun da ke cikin wannan rukuni sun hada da Burundi da Botswana

Kasashe nawa ne za su buga wannan gasa?

Kasashe 12 ne za su buga wannan gasa wadda za ta gudana a Morocco. Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ta rarraba kasashen zuwa rukuni uku dauke da kasashe hudu kowanne.

Rukunin A: Morocco da Burkina Faso da Senegal da kuma Uganda. Rukunin B: Kamaru da Zambia da Tunisia da kuma Togo.

Rukunin C: Najeriya da Afirka ta Kudu da Burundi da kuma Botswana.

A 2021 ba a samu damar gudanar da wannan gasa ba saboda annobar korona.

Gasar da za ta gudana a Arewacin Afrinca, ita ce ta farko da aka buda daga kasashe 8 zuwa 12.

Kasashen da suka zo gasar a karon farko

Kamar ko wacce irin gasa, akan samun kasashen da suke halartar a karon farko.

A wannan shekarar ma an samu wasu kasashen guda hudu da suka zo a karon farko da suka hada da:

• Togo • Burundi • Burkina Faso • Botswana

Wadanne tawagogi ne hankali zai koma kansu?

Kasar da ke kan gaba cikin jerin kasashe ita ce Najeriya, Super Falcons ita ce ta daya a kungiyoyin Afrika ta 39 a duniya.

Gasa uku ta baya da ta gudana Najeriya ce ta lashe, kuma karo tara da ta lashe a jumulla.

Kuma 'yar wasanta mai taka leda a Barcelona Assisat Oshola ita ce ta fi kowacce taka leda a gasar.

Ita ce ta lashe takalmin zinare a babbar gasar tamaula ta mata ta Sifaniya.

Ta ci kwallo 20 cikin wasa 19 da ta buga, kuma an bata kyautar ne tare da 'yar kasar Brazil Geyse Ferreira wadda ta ci kwallo 20 a wasanni 27 da ta yi.

Ta yaya kasashen Afrika za su iya zuwa gasar cin kofin duniya ta 2023?

Kasashe hudu da za su kai karawar daf da karshe a gasar kofin Afirka ta bana, su ne za su wakilci Afirka a gasar kofin duniya ta mata da za a yi a 2023.

Sauran kungiyoyin biyu za su yi wasan samun gurbi ne da za a fafata tsakanin kasashen 10 don halartar World Cup da za a yi a Australia da New Zealand.