Clattenburg zai ja ragamar kwamitin raflin tamaula a Masar

An wallafa

An nada tsohon alkalin gasar Premier League, Mark Clattenburg a matakin wanda zai ja ragamar sabon kwamitin raflin tamaula a Masar da aka kirkira.

An cimma wannan matsaya, bayan kammala taron da hukumar kwallon kafar Masar ta gudanar ranar Laraba.

Hukumar ta yi hakan ne, bayan da kungiyoyin kwallon kafar kasar ke yawan korafi kan yadda rafli ke gudanar da aikinsu a gasar Premier ta Masar ta bana.

A shekarun baya kungiyoyi da yawa sun yi barazanar daina buga gasar kasar, domin nuna bacin ransu kan hukunce-hukuncen da raflin ke yankewa na rashin adalci.

Clattenburg ya hura wasa 570 a Ingila da nahiyar Turai da duniya, tsakanin 2000 zuwa 2017.

Ya nuna kwarewarsa a wasa biyu da ya hura a 2016 a Champions League karawar karshe a Milan da gasar kofin nahiyar Turai tsakanin Portugal da Faransa.

Mai shekara 47, ya bar hura wasannin gasar Ingila a Fabrairun 2017 daga nan ya maye gurbin Howard Webb a Saudi Arabia a matakin shugaban alkalan tamaular kasar.

Clattenburg ya kuma yi aiki a China.