Ko za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza bayan kisan shugaban Hamas?

    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

An fara samun masaniya kan yadda aka kashe Ismael Haniyeh. Alamu dai na nuna cewa shi da masu gadinsa sun mutu ne bayan an kai harin roka kan gidan da yake zama a birnin Tehran.

Kallo dai ya koma kan Isra'ila wadda ta lashi takobin sai ta ga bayan duk wasu shugabannin Hamas bayan harin da aka kai ranar 7 ga watan Oktoba inda aka kashe kimanin mutane 1200.

Isra'ila dai ba ta cika tsokaci kan ayyukan da take gudanarwa a ƙasashen waje ba, amma wannan harin na iya ɗaukar salon wani harin da ta taɓa kaiwa kan matakan tsaron sama da ke kewaye da tashar nukiliyan Iran da ke yankin Natanz a ranar 19 ga watan Afrilu.

Ana tunanin jiragen yaƙin Isra'ilan sun harba rokoki ne daga wajen sararin samaniyar Iran.

Amma yayin da bayanan harin ke ɓullowa a hankali, an ɗan fara ganin alamun tasirinsa kan al'amuran siyasa.

Lamarin da zai fi tasiri a kai shi ne ƙokarin da ake yi na tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Duk da ya ke Haniyeh ba shi ke gudanar da al'amuran yau da kullum na Hamas a Gaza ba - wannan ya faɗa a ƙarƙashin hurumin kwamandan sojin ƙungiyar Yahya Sinwar - amma a matsayinsa na shugaban Hamas da ke gudun hijira ya kasance babban jigo a tattaunawar da Qatar da Amurka da Masar ke shiga tsakani.

A baya bayan nan jami'an gwamnatin Amurka sun yi nuni da cewa ana daf da a cimma yarjejeniya a tattaunawar tsagaita wutar, duk da ya ke taron da aka yi a birnin Roma a makon da ya gabata bai haifar da wata matsaya ba.

Amma zai yi wuya a ga yadda za a samu wani ci gaba a wannan lamarin bayan kisan Ismail Haniyeh.

Me ya sa aka aikata yanzu?

Abin tambaya dai a nan shi ne: Idan wannan kamar yadda kowa ke tsammani aikin Isra'ila ne, Me ya sa aka aikata a yanzu?

Baya ga buƙatarta ta ɗaukar fansa kan duk wani da yake da alaƙa da Hamas, wace manufa ce Isra'ila ke neman ta cimma?

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta riga ta bayyana ra'ayin mutane da dama a yankin.

"An sake bayyanawa ƙarara cewa gwamnatin [Firaministan Isra'ila Benjamin] Netanyahu ba ta da niyyar cimma zaman lafiya," in ji wata sanarwar da ta fitar.

Labarin mutuwar Haniyeh ya janyo matuƙar damuwa a Ramallah, hedikwatar hukumar Falasdinawa.

''Wannan an buɗe taskar tashin hankali ne,'' Sabri Saidam, wanda shi ne mataimakin sakatare janar na kwamitin gudanarwa na jam'iyyar Fatah da ke mulki ya shaida wa BBC.

Mista Saidam ya ce yanayin ya kasance na tashin hankali gauraye da ɓacin rai

''Ba wai na ji kaman Isra'ila na harin rayuwar Ismael Haniyeh ba ne kaɗai, amma tana harin duk wani matsuguni da yake yankin, Isra'ila ta wargaza duk wata fata da ake yi ta kawo ƙarshen wannan rikicin.''

Ƙungiyoyin Fatah da Hamas sun daɗe suna hamayya da juna, wani lokaci har yana kai wa ga artabu tsakaninsu. Amma Mista Saidam ya yi watsi da batun cewa ƙungiyar Fatah ce za ta yi riba daga mutuwar shugaban na Hamas.

''A siyasar Falasɗinu ba a tunanin cewa sai an kawar da wani kafin a yi nasara a harkar shugabanci,'' In ji shi.

''Idan ma akwai wani abu, baƙin jini kawai yake ƙara rurawa tsakanin mu.''

An ƙaddamar da yajin aiki a Ramallah da ɗaukacin yankin gaɓar yamma da kogin Jordan.

An garƙame shaguna kuma ana gudanar da tattakin zanga-zanga, wanda zai iya sanya Hukumar Falasɗinawa da ke Ramallah a tsaka mai wuya.

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan ta nuna cewa Ismael Haniyeh ya fi Shugaban Falasdinu, Mahmud Abbas farin jini a idon al'umma.

Kisan da aka yi wa Haniyeh ya yi nuni cewa wani ɓangare ne na barazanar ɗaukar fansa kan harin roka da ƙungiyar Hezbollah ta kai da ya kashe yara da matasa guda 12 a Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye a ranar Asabar - ramuwar gayya da ta haɗa da kisan wani babban kwamandan Hezbollah a Beirut ranar Talata.

Isra'ila ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki mummunar fansa kan harin.

A lokuta da dama jami'an Isra'ila sun yi nuni da cewa Iran ta kasance wata matattarar masu tayar da ƙayar baya a yankin gabas ta tsakiya, wanda ya haɗa da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon da Hamas a Zirin Gaza da gaɓar yamma da kogin Jordan, da kuma Houthi da ke Yemen.

Bayan yi wa ƙungiyar Hezbullah lahani a Beirut (da kuma kwanan nan ga ƴan Houthi a Hodeidah), kashe shugaban Hamas a Iran ya aika da saƙo mai ban tsoro, ga ƙungiyoyin gwagwarmaya da kuma Iran da ke mara musu baya cewa: Isra'ila za ta iya kai wa gare ku, a duk inda ku ke.