Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba

An wallafa

Kungiyoyin Falasdinawa biyar masu gwagwarmaya da makamai ne suka hada karfi da karfe da Hamas, don kai wa Isra'ila kazamin harin 7 ga watan Oktoba, bayan sun yi ta samun horo a wani atisaye irin na sojoji daga shekara ta 2020, kamar yadda bin diddigin BBC ya nuna.

Kungiyoyin sun rika atisayen ne a Gaza, wanda ya yi iri ɗaya da dabarun da suka yi amfani da shi lokacin da suka kai kazamin hari - ciki har da wani wuri mai nisan kilomita ɗaya daga shingen da ya raba su da Isra'ila - kuma suka wallafa a shafukan sada zumunta.

Sun koyi yadda za su yi garkuwa da mutane, kai samame cikin gidaje da karya matakan tsaron Isra'ila yayin atisayensu nasu, inda suka yi atisayen karshe kwanaki 25 kafin kai harin.

Sashen Larabci na BBC da kuma sashen BBC mai tantance labaran gaskiya sun tattara hujjoji da ke nuna yadda Hamas ta haɗa kan ɓangarorin mayaka a Gaza zuwa wuri ɗaya domin cimma burinsu - na kaddamar da hari zuwa cikin Isra'ila wanda ya jefa yankin cikin yaƙi.

'Alamar haɗin kai'

A ranar 29 ga watan Disamban 2020, jagoran ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya ayyana atisayen farko cikin atisaye huɗu da "babban sako da alamar haɗin kai" tsakanin ƙungiyoyin mayaka daban-daban a Gaza.

Kasancewarta ƙungiyar mayaka mafi girma a Gaza, Hamas ita ce ja-gaba wajen haɗakar wadda ta kawo ƙungiyoyin mayaka goma zuwa wuri ɗaya, a wani shirin yaƙi da suka yi.

An kirkiro da tsarin ne a 2018 domin haɗa kan ƙungiyoyin mayaka daban-daban a Gaza zuwa karkashin iko ɗaya.

Kafin 2018, Hamas ta riga da haɗa kai da ƙungiyar mayaka ta Falasɗinawa ta Islamic Jihad(PIJ), wadda ta kasance ƙungiya ta biyu mafi girma a Gaza - kamar Hamas - wadda Amurka da wasu ƙasashe suka ayyana a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda.

Hamas da wasu ƙungiyoyi sun shiga rikicin da aka yi a baya, sai dai atisayen 2020 yana cike da farfaganda kamar yadda ake gani wajen haɗin kai tsakanin ƙungiyoyi da dama.

Shugaban Hamas ya ce atisaye na farko ya nuna shirin da ɓangarorin mayaka Falasɗinawa suka yi.

Atisayen na shekara ta 2020 na ɗaya daga cikin atisaye huɗu da aka gudanar cikin shekaru uku, inda aka naɗi dukkan hotunan bidiyon atisayen da kuma yaɗa su a shafukan sada zumunta.

BBC ta kai ga gano ƙungiyoyin mayaka goma, ciki har da PIJ, ta hanyar alamun ɗaurin kyalle a kai da kuma wata alama tare da ƙungiyar Hamas lokacin wani atisaye wanda aka wallafa a shafin Telegram.

Bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, ƙungiyoyin mayaka biyar sun wallafa hotunan bidiyo da ya nuna sun taimaka wajen kai harin. Wasu uku kuma sun fitar da sanarwa a shafin Telegram da suke iƙirarin hannunsu a kaddamar da harin.

An fuskanci yadda irin rawar da waɗannan ƙungiyoyi suka taka a daidai lokacin da matsin lamba ke ƙaruwa kan Hamas don nemo gomman mata da yara da aka yi imanin cewa sun yi garkuwa da su daga Isra'ila zuwa cikin Gaza tare da haɗin gwiwar wasu ɓangarori na ƙungiyoyin mayaka Falasɗinawa a ranar 7 ga Oktoba.

Ƙungiyoyi uku - PIJ, Mujahideen Brigades da Al-Nasser Salah al-Deen Brigades - sun yi iƙirarin cewa su da Hamas ne suka yi garkuwa da mutanen Isra'ila a ranar da suka kai hari.

An ce ƙoƙarin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi a Gaza ta dogara ne kan Hamas na sakin dukkan waɗanda ta yi garkuwa da su.

Shaidar ƙungiyoyi biyar da suka haɗu suka kai harin 7 ga watan Oktoba da Hamas

Duk da yake waɗannan ƙungiyoyin sun fito ne daga akidoji daban-daban na masu tsattsauran ra'ayin Islama zuwa waɗanda ba su da addini, duk suna da niyyar yin amfani da tashin hankali kan Isra'ila.

Sanarwar Hamas ta sha jaddada taken haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Gaza. Ƙungiyar ta bayar da shawarar cewa su kasance abokan haɗin gwiwa a atisayen da za su yi, yayin da ta ci gaba da taka rawa a shirye-shiryen kai wa Isra'ila hari.

Hotunan bidiyo na atisayen farko sun nuna kwamandojin da suka rufe fuskokinsu a cikin wani wuri da ke nuna cewa suna gudanar da atisayen, kuma sun fara da harbin roka.

Ta kai ga wasu mayaka na ɗauke da muggan makamai da suka mamaye wata tanka mai ɗauke da tutar Isra'ila, tare da tsare wani ma'aikacin jirgin tare da jan shi a matsayin fursuna, da kai farmaki kan gine-gine.

Mun san daga hotunan bidiyo da shaidu masu ban tsoro cewa duka dabarun biyu an yi amfani da su ne wajen kame sojoji tare da kai wa fararen hula hari a ranar 7 ga Oktoba, lokacin da aka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da kusan 240.

Faɗa wa duniya

An gudanar da atisaye na biyu mafi girma kusan shekara ɗaya bayan nan.

Ayman Nofal, wani kwamandan ƙungiyar mayaka ta Izzedine al-Qassam Brigades - sunan wani ɓangare na Hamas - ya ce niyyar atisayen na ranar 26 ga watan Disamban 2021 shi ne "assasa haɗin kai na ƙungiyoyin".

Ya ce atisayen zai "fada wa abokan gaba cewa ganuwar da matakan zamani a kan iyakokin Gaza ba za su kare su ba".

Wata sanarwar da Hamas ta fitar ta ce, "tattakin haɗin gwiwa na soji" an yi shi ne don "kwato 'yancin matsugunan da ke kusa da Gaza" - abin da ƙungiyar ke nufi ga al'ummomin Isra'ila.

An sake yin atisayen ne a ranar 28 ga Disamba 2022, kuma an wallafa hotunan farfaganda na mayaka da ke aikin ruguza gine-gine da kuma tankokin yaƙi a cikin abin da ya zama maimaici na irin sansanin soji don murnar bikin.

An ruwaito batun atisayen a cikin Isra'ila, don haka abin mamaki ne ganin cewa ba a bi diddiginsu ba daga Isra'ila da ta kasance ƙasa mafi kwararrun hukumomin tattara bayanan sirri a duniya.

A baya, dakarun tsaron Isra'ila sun kai hare-hare ta sama domin kawo wa Hamas cikas a atisayenta. A watan Afrilun 2023, sun tayar da bam a wuri na farko da Hamas ta yi atisaye.

Makonni kafin kai harin, sojoji mata masu sa ido a kusa da iyaka da Gaza sun yi gargaɗin cewa sun ga ayyukan wani jirgi maras matuki ya yawaita kuma Hamas na yin atisaye don karɓe iko da shingayen sa ido.

Sai dai, a cewar rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Isra'ila, sun ce ba a yi komai kan gargaɗin ba.

Birgediya Janar Amir Avivi, wani tsohon kwamandan dakarun ƙasar a Gaza, ya faɗa wa BBC cewa: "Akwai bayanan sirri da dama da suka nuna suna gudanar da wannan atisaye - baya ga haka, hotunan bidiyon sun karaɗe ko'ina, kuma hakan na faruwa ne mitoci kaɗan daga iyaka da Isra'ilar.

Sai dai, ya ce yayin da sojoji suka san da batun atisayen, ba su gane a kan me Hamas ɗin ke atisaye ba.

Dakarun tsaron ƙasar sun ce sun kashe Nofal a ranar 17 ga watan Oktoban 2023, babban jami'in Hamas na farko da aka kashe lokacin rikicin.

Ɓuya a wuraren da za a iya gani

Hamas ta kai kololuwa wajen tabbatar da cewa atisayen ya cimma nasara.

A 2022, mayakan ƙungiyar sun koyi yadda suka far wa wani sansanin sojin Isra'ila da aka kafa kilomitoci 2.6 daga Erez, hanyar da ta haɗa Gaza da Isra'ila wadda dakarun tsaron Isra'ila ke iko da ita.

Sashen BBC mai tantance labaran gaskiya ya gano wurin a can nesa da arewacin Gaza, mitoci 800 daga shingen, ta hanyar haɗa hotuna da aka gani a wurin atisayen. Zuwa watan Nuwamban 2023, wurin ya ci gaba da kasancewa a taswirar Bing.

Sansanin bayar da horon yana da nisan kilomita ɗaya da rabi da wata hasumiyar sanya ido ta Isra'ila, wadda ta kashe miliyoyin dalolin Amurka wajen ginawa.

Sansanin sojoji na gwaji yana kan ƙasar da aka haƙa mita da yawa a ƙarƙashin ƙasa, don haka da wuya jami'an sintiri na Isra'ila da ke kusa sun gano wurin - amma hayaƙin da ke tashi daga ababen fashewa zai iya sa su gani, kuma an san cewa dakarun tsaron Isra'ila na sa ido ta sama.

Hamas ta yi amfani da wannan wuri wajen gudanar da ayyukan kai farmaki kan gine-gine, da yin garkuwa da su da bindiga da kuma lalata shingen tsaro.

Sashen BBC mai tantance labaran gaskiya ya yi amfani da bayanan da ake samu a bainar jama'a - ciki har da hotunan tauraron ɗan adam - don gano wuraren horo 14 a wurare daban-daban guda tara a faɗin Gaza.

Har ma sun yi horo sau biyu a wani wuri da bai wuce kilomita ɗaya da rabi ba daga cibiyar rarraba kayan agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda kuma aka gani a bayan wani hoton bidiyo da hukumar ta wallafa a watan Disamba 2022.

Kai hari ta ƙasa, ruwa, da kuma sama

A ranar 10 ga Satumba 2023, wani ɗakin kwamitin haɗin gwiwa ya wallafa hotuna a shafin Telegram na maza sanye da kakin soji da ke aikin sa ido kan ayyukan soja a kan shingen Gaza.

Bayan kwana biyu, an gudanar da atisayen soji na huɗu, kuma a ranar 7 ga Oktoba, an sake nazarin duk dabarun da za a yi amfani da su a harin da ba a taɓa gani ba.

An ɗauki hoton mayaƙan suna tafiya a cikin fararen motoci kirar Toyota da aka gani suna yawo a kudancin Isra'ila a wata guda bayan nan.

Bidiyon farfagandar ya nuna yadda wasu ‘yan bindiga ke kai farmaki kan gine-ginen gwaji da harbe-harbe, da kuma horar da su a kan yadda za su far wa gaɓar teku ta hanyar amfani da kwale-kwale da masu ninƙaya.

Isra'ila ta ce ta dakile yunkurin saukar kwale-kwalen Hamas a gaɓar ruwanta a ranar 7 ga watan Oktoba.

Sai dai, Hamas ba ta wallafa batun horonta da babura da masu saukar lema a matsayin wani ɓangare na farfagandar atisayen Strong Pillar ba.

Bidiyon horon da Hamas ta wallafa kwanaki uku bayan 7 ga Oktoba ya nuna shingen da ake ruguzawa don bai wa baburori damar wucewa, dabarar da suke amfani da ita don isa ga al'ummomin kudancin Isra'ila.

Ba mu gano irin waɗannan hotunan bidiyo ba a farko.

Har ila yau, ba a wallafa bidiyon mayaka da ke amfani da na'urorin motsa jiki ba har sai da aka kai harin na ranar 7 ga Oktoba.

A cikin wani bidiyo na horo da aka yaɗa a ranar da aka kai harin, an ga wasu ‘yan bindiga suna sauka a wani wurin gwaji a yankin kibbutz a filin jirgin sama da muka gano zuwa wani wuri da ke arewacin Rafah a kudancin Gaza.

Sashen BBC mai tantance labaran gaskiya ya tabbatar da cewa an naɗi bidiyon a wani lokaci kafin 25 ga Agustan 2022, kuma an adana shi a kwamfuta mai suna Eagle Squadron, sunan da Hamas ke amfani da shi don kai samame ta iska - yana nuna cewa shirin masu saukar lema yana kan aiki sama da shekara guda.

Harin ba-zata

Kafin ranar 7 ga Oktoba, ana tunanin Hamas na da mayaka kusan 30,000 a Zirin Gaza, a cewar rahotannin da ke ambato kwamandojin Isra'ila.

An kuma yi imanin cewa Hamas ɗin za ta iya jawo dubban mayaka daga ƙananan ƙungiyoyi.

Hamas ita ce mafi karfi a cikin ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ɗauke da makamai, ko da ba tare da samun goyon bayan wasu ɓangarori ba.

A baya dai rundunar ta IDF ta kiyasta cewa mayaka 1,500 ne suka shiga farmakin na ranar 7 ga Oktoba.

Jaridar Times ta Isra’la ta ruwaito a farkon wannan watan cewa yanzu dakarun tsaron ƙasar sun yi imanin cewa adadin ya kusa 3,000.

Ko mene ne adadin na gaskiya, yana nufin kaɗan ne kawai na adadin ma'aikatan da ke ɗauke da makamai a Gaza suka shiga yakin.

Ba zai yiwu a iya tantance takamaiman adadin mayaka daga ƙananan ƙungiyoyi nawa ne suka shiga harin ba ko kuma atisayen na Strong Pillar.

A yayin da ƙungiyar Hamas ke ci gaba da samun goyon bayan ɓangarorin biyu wajen tunkarar harin, Hisham Jaber, tsohon Birgediya Janar a rundunar sojin Lebanon wanda a yanzu shi ne mai sharhi kan harkokin tsaro a cibiyar nazari da bincike ta Gabas ta Tsakiya, ya ce ya yi imanin cewa Hamas ce kawai ke sane da shirin kai harin, kuma ya kasance "mai yiyuwa ne su nemi wasu ƙungiyoyi su shiga a ranar.

Andreas Krieg, babban malami a fannin nazarin harkokin tsaro a Kwalejin Kings da ke Landan, ya shaida wa BBC cewa: "Duk da cewa akwai tsare-tsare a ƙasa, an yanke hukuncin kisa a tsaka-tsaki, inda kowace tawagar ta aiwatar da shirin yadda ta ga dama."

Ya ce mutanen da ke cikin ƙungiyar Hamas sun yi mamakin raunin tsaron da Isra'ila ke da shi, kuma ya yi kiyasin cewa mayakan sun keta fasahar sa ido ta Isra'ila ta hanyar tattaunawa a ɓoye ba tare da amfani da intanet ba.

Hugh Lovatt, wani manazarci a Gabas ta Tsakiya a Majalisar Tarayyar Turai kan Harkokin Waje, ya ce da Isra'ila ta san da atisayen haɗin gwiwa amma "ta cimma matsaya mara kyau", yana mai kiyasta cewa sun yi daidai da ayyukan ƙungiyoyin sa kai a yankunan Falasɗinawa, maimakon zama "mai nuni ga babban hari da ake shirin kai wa".

Da aka tambaye shi game da batutuwan da aka gabatar a wannan labarin, rundunar tsaron Isra'ila ta ce "a halin yanzu ta mayar da hankali kan kawar da barazanar ƙungiyar ta'addanci ta Hamas" kuma tambayoyi game da duk wata gazawar da za a iya samu "za a duba su a wani mataki na gaba".

Yana iya zama shekaru da yawa kafin har sai Isra'ila ta yi la'akari da ko ta rasa damar da za ta hana kisan kiyashin 7 ga Oktoba.