Ko Yamal zai taka rawa a lamba 19 da Barcelona ta sauya daga 27?

Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Lamine Yamal zai saka riga mai lamba 19 a kakar 2024/25 a Barcelona, lambar da Patrick Kluivert da Leo Messi da Sergio Aguero suka yi amfani da ita a baya.

Ɗan wasan zai bi sawun fitattun ƴan ƙwallon ƙungiyar da suka taka rawar gani a Barcelona, kuma lambar da ya yi amfani da ita kenan a Euro 2024 a tawagar Sifaniya.

Sifaniya, wadda ta lashe Euro 2024 ta ɗauki kofi na hudu jimilla, babu wadda ta ɗauki kofin da yawa kamarta, kuma Yamal ne matashin da ya yi fice a wasannin da aka yi a Jamus.

Ɗan wasa Vitor Rogue ne ya saka lamba 19 a bara a Barcelona, kuma lamba ce da matasa da yawa da fitattun da suka yi amfani da ita tun daga 1995.

Jerin waɗanda suka yi amfani da lamba 19 a Barcelona:

  • Lluís Carreras (1995/96)
  • Juan Antonio Pizzi (1996-98)
  • Patrick Kluivert (1998/99)
  • Dani Garcia Lara (1999-03)
  • Fernando Navarro (2004/05)
  • Leo Messi (2005-08)
  • Maxwell (2009-12)
  • Martín Montoya (2012/13)
  • Ibrahim Afellay (2013/14)
  • Sandro Ramírez (2015/16)
  • Lucas Digne (2016-18)
  • Munir El Haddadi (2018)
  • Kevin-Prince Boateng (2019)
  • Carles Aleñá (2019)
  • Martin Braithwaite (2020)
  • Matheus Fernandes (2020/21)
  • Kun Aguero (2021)
  • Ferran Torres (2022)
  • Franck Kessie (2022/23)
  • Vitor Roque, (2023/24)

Lamine ya cika shekara 17 da haihuwa ranar 13 ga watan Yulin 2024, ya saka riga riga mai lamba 27 a bara a Barcelona.

A karkashin koci, Xabi Hernandez a 2023/24 ya buga wasa 50, inda Ilkay Gündoğan ne kan gaba a yawan yi wa ƙungiyar wasanni a bara mai 51.