Su wane ne ƴan Najeriya suka zaɓa?

...
An wallafa

A ranar 25 ga watan Fabarairu ne al'ummar Najeriya suka yi tururuwa zuwa rumfunan kaɗa ƙuri'a don zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisun dokoki na tarayya.

Sannan a ranar 18 ga watan Maris suka sake komawa domin zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar dokokin jihohi.

Shin ya sakamakon zaɓen ya kasance?

BBC ta tsamo waɗannan alƙaluma inda ta ɗora su a taswira don sauƙaƙa muku fahimta.

Yawan gwamnonin jihohin da kowace jam'iyya ta samu

.

Bayan zaɓen gwamnoni na ranar 18 ga watan Fabrairu, sakamakon zaɓe da hukumar INEC ta fitar ya nuna cewa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ce ta samu kujerun gwamnoni mafi yawa.

APC ɗin ta lashe jihohi 15, PDP ta samu tara, NNPP na da ɗaya, haka nan ma LP na da ɗaya.

Sai dai an bayyana zaɓen gwama a jihohin Adamawa da Kebbi da cewa ba su kammala ba.

Wace jam'iyya ce ta fi cin kujerun Sanatoci?

...

Sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana ya nuna cewa jam'iyyar APC ce take da rinjaye a majalisar dattijai, inda ta samu kujeru 55.

PDP ce take bi mata da kujeru 33, yayin da LP take da kujeru bakwai, sai NNPP wadda ke da kujeru biyu.

Sai kuma sauran jam'iyyu waɗanda jumulla suka yi nasarar samun kujeru huɗu.

Sai dai akwai kujeru takwas da ba a bayyana sakamakon zaɓensu ba, waɗanda daga cikinsu za a sake zaɓe.

Majalisar Wakilan Tarayya

...

Sakamakon zaɓen majalisar wakilai, ya nuna cewa babu jam'iyyar da ke da rinjaye, kasancewar dole ne sai jam'iyya ta samu yawan kujerun da suka zarce kashi 51 cikin ɗari na jumullar kujerun majalisar 360, kafin a ce ta samu rinjaye.

Duk da haka, jam'iyyar APC ce ke kan gaba a yawan kujerun majalisar bayan cin zaɓen mazaɓu 159.

Sai jama'iyyar PDP wadda ta zo a mataki na biyu da kujeru 104, sai LP mai kujeru 35, NNPP kujera 18, sauran jam'iyyu suna da kujeru 9, akwai kuma sauran mazaɓu 35 da ba a kammala zaɓensu ba.

Jimillar ƙuri'un da kowace jam'iyya ta samu a zaɓen gwamnonin jihohi da kuma na shugaban ƙasa

...

Ƙuri'un da jam'iyyun APC da PDP da kuma NNPP suka samu a zaɓen gwamnoni sun ɗara yawan waɗanda suka samu a zaɓen shugaban ƙasa.

Sai dai ita jam'iyyar LP ta samu raguwar yawn ƙuri'u a lokacin zaɓen gwamna idan aka kwatanta da abin da ta samu a zaɓen shugaban ƙasa.

Jihohin da mutane suka fi fitowa kaɗa ƙuri'a

...

Alƙaluma sun nuna cewa an samu ci gaba a yawan mutanen da suka fito kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnoni idan aka kwatanta da zaɓen shugaban ƙasa wanda aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kuma jihohin da mutane suka fi fitowa domin kaɗa ƙuri'a su ne Jigawa da Zamfara da kuma Filato.

Yayin da jihohin da aka fi samun ƙaramcin fitowar masu zaɓe su ne Ribas da Enugu da kuma Lagos.