Maguire ya jinjina wa David Beckham

An wallafa

Tsohon Kyaftin ɗin Manchester United Harry Maguire ya ce kiran da David Beckham ya yi masa bayan wasan Ingila da Scotland ya taimaka masa wurin farfaɗowa daga sukar da ya ke sha kan kura-kuran da ya ke yi.

Ɗan wasan bayan na Ingila ya ci gida a wasan sada zumunta da suka doke Scotland da ci 3-1 a watan da ya gabata a Glasgow.

Maguire ya ƙara da cewa: “Ya tunatar da ni kan irin nasarorin da na samu a wasan ƙwallon kafa da kuma rayuwata baki ɗaya.

Maguire, wanda shi ne ɗan wasan baya mafi tsada a duniya lokacin da ya koma Manchester United daga Leicester da aka saya fam miliyan 80 a shekarar 2019, ya buga wa Ingila wasanni 59 kuma ya ci ƙwallaye bakwai.

Amma ya sami ƙalubale wurin samun lokacin wasa a Old Trafford tun lokacin da aka naɗa Erik ten Hag a matsayin koci a 2022 - inda har ma aka karɓe muƙamin kyaftin daga hannunsa.

Maguire ya kusa komawa West Ham a bazarar da ta wuce bayan an amince da yarjejeniyar fam miliyan 30 tsakanin ƙungiyoyin biyu, amma ya zaɓi ya zauna ya fafata a ƙungiyar domin ƙwato gurbin wasansa.

Maguire ya ce ya san cewa 'yan wasa da dama na shan suka duk da ƙwarewarsu a wasan kwallo.

Mai tsaron bayan ya ƙara da cewa yadda kocin Ingila Gareth Southgate da takwarorinsa suka ɗauke shi ya sa ya ji cewa yana da muhimmanci.