Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zan bai wa matasa dama a Man United a bana - Ten Hag
Erik ten Hag ya bukaci matasan Manchester United da su kara kwazo su karbi gurbi a kungiyar tun kan fara kakar bana.
A makon gobe ne United za ta fara kakar bana da Community Shield, inda za ta fafata da Manchester City a Wembley.
Kungiyar Old Trafford, wadda za ta kara a Europa League a 2024/25, na fatan taka rawar gani a Premier League da FA Cup da kuma League Cup.
Ten Hag ya ce yadda aka tsara kalandar wasanni ta bana, za ta bai wa matasan 'yan wasa damar buga wa kungiyoyinsu wasanni.
Harry Amass da Toby Collyer duk sun fara wasannin da United ta yi a Amurka na tunkarar kakar bana, sai dai wasu na cewa da kyar ne idan za ake saka su a fafatawar kakar da za a fara cikin watan Agusta.
To sai dai kociyan ya ce zai bai wa duk wani matashin kungiyar dama da zarar ya nuna kwazo da jajircewa a bana.
Manchester United ta ci karo da koma baya a kakar da ta wuce, wadda ta dauki FA Cup, bayan doke Manchester City a Wembley a kakar da ta wuce.
Sakamakon wasannin sada zumunta na Man United
15 ga watan Yuli Rosenborg 1-0 Man Utd
20 ga watan Yuli Rangers 0-2 Man Utd
28 ga watan Yuli Arsenal 2-1 Man Utd
1 ga watan Agusta. Man Utd 3-2 Real Betis
4 ga watan Agusta Man United da Liverpool (South Carolina)
10 ga watan Agusta Man United da Man City (Wembley) FA Community Shield