Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas
- Marubuci, By Yolande Knell & David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, in Jerusalem and London
- An wallafa
Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar musayar mutum 50 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma tsagaita buɗe wuta na tsawon kwanaki hudu a yaƙin da suke yi.
A cikin yarjejeniyar kuma za a saki Falasdinawa 150 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila da kuma ƙaruwar taimakon jin-ƙai da aka ba su izinin shiga Gaza.
Mai shiga tsakani, Qatar ta ce yarjejeniyar za ta soma aiki ne da ƙarfe 07:00 agogon Gaza, ranar Juma'a kuma za a sako rukunin farko na mutane 13 da aka yi garkuwa da su da karfe 4:00.
Shugaban Amurka ya ce yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen matsalolin da masu garkuwar ke fuskanta da kuma "rage raɗaɗin wahalhalun ga iyalan Falasdinawa da ba su ji ba su gani ba."
Gwamnatin Isra'ila ta sha alwashin kammala yaƙinta na kawar da kungiyar Hamas tare da ceto sauran sama da mutane 200 da ƴan bindigar Hamas suka yi garkuwa da su a wani harin wuce gona da iri kan kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe mutane 1,200.
Kungiyar Hamas - wadda Isra'ila da Amurka da sauran kasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin kungiyar ƴan ta'adda - ta ce yarjejeniyar za ta bai wa Falasdinawa lokaci don farfadowa bayan kazaman hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da ta kasa da gwamnatinta a Gaza ta ce sun yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 14,500.
Waɗanne mutanen da aka yi garkuwa da su za a sako?
Ba a buga sunayensu ba, amma mun san cewa dukkansu za su kasance mata da yara.
Bayan da gwamnatin hadin gwiwa ta Isra'ila ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya da sanyin safiyar Laraba, ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa "za a sako aƙalla mutane 50 da aka yi garkuwa da su - mata da yara cikin kwanaki hudu, inda za a dakatar da fadan. ".
Har ila yau, ta bai wa Hamas ƙwarin gwiwar ƙarin sakin wasu, tana mai cewa: "Sakin kowane ƙarin mutane 10 da aka yi garkuwa da su zai haifar da ƙarin kwana guda na tsagaita wuta."
Wannan batu dai yana da matuƙar muhimmanci ga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, waɗanda a baya wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa ba sa son ganin yarjejeniyar ta kasance na wucin-gadi.
Mutanen 50 da ake sa ran za a sako, za a sako su ne rukuni-rukuni har huɗu, kuma yawancinsu ƴan kasar Isra'ila ne da kuma masu izinin zama a wasu ƙasashen waje.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya shaida wa manema labarai a birnin Doha da yammacin jiya Alhamis cewa, rukunin farko na wadanda aka yi garkuwa da su da za a sako a ranar Juma'a za su ƙunshi yara da mata 13, wasu daga cikin su tsofaffi ne.
Majid al-Ansari ya ce: "Za a haɗa waɗanda aka yi garkuwa da su daga dangi daya a rukuni guda."
Ya kuma ce an miƙa jerin sunayen rukunin farko ga hukumar tattara bayanan sirrin Isra'ila ta Mossad don saukaka aiwatar da yarjejeniyar.
Daga baya ofishin Netanyahu ya tabbatar da cewa jami'ai na "bincika bayanan jerin sunayen kuma a halin yanzu suna tuntubar dukkan iyalan".
Wani babban jami'in Amurka ya faɗa a ranar Laraba cewa aƙalla Amurkawa uku - ciki har da Avigail Idan, mai shekaru uku, ɗan kasar Isra'ila mai izinin zama a ƙasashe biyu da aka kashe iyayensa a garin Kfar Aza - za su kasance cikin waɗanda aka yi garkuwa da su 50 da za a sako.
Wani babban jami'in Isra'ila ya faɗa a yammacin ranar Talata cewa, Hamas za ta iya sakin 'yan kasar Thailand su 26 ba tare da ɓata lokaci ba.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ce aka amince a matsayin wadda za ta karɓi mutanen da za a sako daga Gaza, kamar yadda ma’aikatanta suka yi a lokacin da ƙungiyar Hamas ta sako wasu mata ƴan Isra’ila-Amurkawa da wasu mata biyu ƴan Isra’ila a watan jiya.
A daren Laraba, Netanyahu ya ambato yarjejeniyar yana cewa "za a kuma wakilta hukumar ICRC ta karɓi waɗanda aka sako da kuma ba su magungunan da suke buƙata". Sai dai Ansari ya kasa bayyana ko gaskiya ne hakan.
Sojojin Isra'ila da ke aiki a cikin Gaza sun kuma kubutar da wata soja guda tare da ƙwato gawarwakin wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su - soja ɗaya da farar hula ɗaya.
Gwamnatin Isra'ila ta ce za ta ci gaba da yaƙin domin ta kuɓutar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma kammala kawar da ƙungiyar Hamas da kuma tabbatar da cewa ba za a sake samun wata sabuwar barazana ga ƙasar Isra'ila daga Gaza ba.
Me zai faru a Gaza idan yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki?
Sanarwar da ƙungiyar Hamas ta fitar a ranar Laraba ta yi ƙarin bayani kan daina daukar matakin soji na Isra'ila na tsawon abin da ta kira "hudna", ko kuma tsagaita buɗe wuta na wucin-gadi.
Ta ce ana sa ran dukkan ayyukan jirage marasa matuka na Isra'ila za su tsaya na tsawon kwanaki huɗu a kudancin Gaza.
Sai dai a arewacin ƙasar - wanda shi ne wurin da Isra'ila ta fi kai hare-hare domin wargaza kungiyar Hamas - tsagaita buɗe wutan zai kasance ne tsakanin karfe 10:00 na safiya zuwa 4:00 na yamma agogon yankin a kowace rana.
Ana sa ran sojojin Isra'ila da tankunan yaƙi za su ci gaba da kasancewa a wuraren da suke a cikin Gaza a tsawon kwanaki huɗun da za a yi, amma sanarwar Hamas ta ce sojojin Isra'ila ba za su kai hari ko kama wani ba.
Ansari ya ce za a yi “cikakkiyar tsagaita bude wuta” a arewaci da kudancin Gaza, yayin da babban mai shiga tsakani na Qatar, ministan harkokin wajen ƙasar Mohammed al-Khulaifi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “ba za a kai hari ko kaɗan ba, babu komai".
Sassautawar da ake gani yanzu na tsagaita buɗe wuta shine babban burin Falasdinawa a Gaza, wanda miliyan 1.7 daga cikinsu sun tsere daga gidajensu a cewar Majalisar Dinkin Duniya, sakamakon yaƙin tsakanin Isra'ila da Hamas.
Yarjejeniyar dai za ta ba da damar manyan motoci 200 da ke dauke da kayan agaji, da tankunan mai guda hudu, da manyan motoci hudu dauke da iskar gas su shiga Gaza ta mashigar Rafah ta Masar a kowane cikin kwanaki hudun.
Amma an fahimci cewa man fetur - wanda ake buƙata don samar da wutar janareta na asibiti, tsaftace ruwa da najasa - zai dawwama na tsawon lokacin da aka dauka na tsagaita wuta.
Ansari ya ce ƙarin tallafin zai fara shiga cikin Gaza da wuri bayan yarjejeniyar ta soma aiki da safiyar Juma'a kuma an samu kwanciyar hankali da ya sanya aka samu tsaro ga masu aikin jin kai.
Isra'ila ta katse wutar lantarki da mafi yawan ruwa, sannan ta dakatar da kai kayan abinci, man fetur da sauran kayayyaki zuwa Gaza a matsayin ramuwar gayya ga harin Hamas.
Ya ba da damar tireloli 1,399 na kayayyakin jin kai shiga ta Masar tsakanin 21 ga Oktoba da 21 ga Nuwamba, idan aka kwatanta da matsakaicin 10,000 a kowane wata kafin yakin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Ta hana dukkan man da ake kai wa har zuwa makon da ya gabata, tana mai cewa kungiyar Hamas za ta iya sace wa ta kuma yi amfani da shi wajen ayyukan soji.
Kuma ko da yake yarjejeniyar za ta bai wa mutanen Gaza damar wucewa lafiya daga arewa zuwa kudu, ba za ta bari dubunnan daruruwan mutanen da suka rasa matsugunansu daga arewa su koma gida ba.
Su wane ne fursunonin Falasdinawa?
Hamas ta ce yarjejeniyar za ta kuma sa Isra'ila ta saki fursunonin Falasdinawa 150 - dukkansu mata da yara.
Sanarwar da gwamnatin Isra'ila ta fitar ba ta ambaci hakan ba, amma a safiyar Laraba ma'aikatar shari'ar ta ta fitar da jerin sunayen fursunoni 300 da suka cancanci a sake su a cikin harshen yahudanci - bisa yiwuwar ƙungiyar Hamas za ta amince da sakin wasu mutane 50 da aka yi garkuwa da su.
Jerin sunayen ya kunshi yara maza 123 masu shekaru tsakanin 14 zuwa 17, da yarinya ɗaya mai shekara 15, sai maza manya guda 144 masu shekaru 18, da kuma mata 32 masu shekaru tsakanin 18 zuwa 59. Yawancin su ana tsare da su a gidan yari yayin da suke jiran shari'a kan tuhume-tuhumen da suka hada da jifa da duwatsu zuwa yunƙurin kisan kai.
Dalilin da ya sa ya zama dole a buga jerin sunayen shine saboda tsarin doka a Isra'ila. Kafin duk wani sakin fursuna, dole ne a ba wa 'yan Isra'ila izinin sa'o'i 24 domin yin ƙara zuwa Kotun ƙoli ta Isra'ila.
Ansari ya ce Qatar ba za ta iya bayyana wani cikakken bayani game da fursunonin Falasdinawa ba ko nawa za a sako a ranar farko. Amma ya ba da shawarar cewa za a saki mutanen a daidai lokacin da da za a sako waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza.
A halin yanzu dai Isra'ila na tsare da Falasdinawa kusan 7,000 da ake zargi ko kuma aka samu da laifukan tsaro a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin Isra'ila da Falasdinawa.
Kusan Falasdinawa 3,000 ne aka bayar da rahoton cewa an kama su a yankin Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gabashin Ƙudus, inda kuma aka yi tashe-tashen hankula, tun ranar 7 ga Oktoba.
Sanarwar ta Hamas ta ƙare da cewa yarjejeniyar tana da nufin "yi wa jama'armu hidima da kuma karfafa tsayin daka wajen fuskantar ta'addanci".
Har ila yau, ta yi gargadin: "Yatsunmu na kan gaba, kuma mayaƙanmu da suka yi nasara za su ci gaba da sa ido don kare mutanenmu da kuma fatattakar ta'addanci."
Ta yaya za a sanya ido kan yarjejeniyar?
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya ce wani dakin gudanar da ayyuka a Doha zai kula da hanyoyin sadarwa na hakika tare da Isra'ila da ofishin siyasa na Hamas, da kuma ƙungiyar Red Cross (ICRC), ta yadda za a sanar da duk wani abin da zai iya faruwa nan take ga bangarorin biyu kuma akwai hanyar komawa baya daga ciki".
Abu mafi mahimmanci shi ne "tabbatar da cewa yanayin da za a yi musayar mutanen da aka yi garkuwa da su zai kasance cikin lafiya da kwanciyar hankali," in ji shi.
Ansari ya ce Qatar na fatan tsawaita tsagaita buɗe wutan fiye da kwanaki hudun da aka amince ta hanyar tabbatar da sakin wasu mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ya kuma bayyana fatan hakan zai kasance a matsayin "tabbacin ra'ayi na ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace... da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a Gaza".