'Yan Real Madrid da suka je Athletic Bilbao buga La Liga

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta ziyarci Athletic Bilbao, domin buga wasan mako na 18 a gasar La Liga ranar Lahadi.

Real Madrid, wadda ta je filin wasa na San Mammes tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona ta daya.

Athletic mai maki 26 tana ta takwas a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya a bana.

Ranar Alhamis Real Madrid ta je ta doke Villareal 3-2 a Copa del Rey karawar zagayen kungiyoyi 19.

Real Madrid wadda ta fara daukar European Super Cup a bana ta yi rashin nasarar lashe Spanish Super Cup, bayan da Barcelona ta doke ta 3-1 a Saudi Arabia. 

'Yan wasan Real da suka je Athletic:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis López.

Masu tsaron baya: E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.