Adrien Rabiot ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi a Juventus

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Dan wasan tsakiyar Adrien Rabiot ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi a Juventus.
Dan wasan mai shekara 28 dama kwantaraginsa za ta are ne a wannan kakar, kuma tuni Manchester United ta fara nuna sha'awarta game da shi.
Rabiot ya koma Juventus ne a kakar 2019 bayan ya baro Paris St-Germain kuma ya buga mata wasa 177 ya ci kwallo 17.
Ya taimakawa ƙungiyar ta kai ga lashe kofin Serie A a 2019-20.
Raboit wanda ya lashe kofin Italiya da Supercoppa lokacin zamansa a Juventus, ya ci kwallo 11 a bara ya kuma bayar an ci shida.
Ya taimakawa Faransa ta kai wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2022, wanda aka cinye ƙasarsa a bugun fenareti da ta yi da Argentina.







