Zakaƙurin ɗan wasan Italiya Schillaci ya mutu

Schillaci

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Fitatcen ɗan wasan tawagar Italiya, Salvatore Schillaci, wanda ya lashe ƙyautar yawan cin ƙwallo a kofin duniya a 1990 ya mutu yana da shekara 59 da haihuwa.

Schillaci, wanda aka fi sani da suna 'Toto' ya ci ƙwallo shida, wanda ya lashe takalmin zinare a gasar kofin duniya a 1990 a Italiya.

Italiya ta yi rashin nasara a daf da karshe a gasar da ta shirya, amma Schillaci ne ya zama fitatcen ɗan wasa.

Ya buga wa kasarsa wasa 16 da cin ƙwallo bakwai, wanda ya taka leda a Juventus da Inter Milan, ya fara taka leda a Messina.

Shi ne na farko ɗan kasar Italiya da ya fara buga tamaula a gasar Japan, wato J-League daga baya ya yi ritaya a1999.