Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko Abdallah zai fitar da Pillars daga halin da take ciki?
- Marubuci, Muhammad Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Kano Pillars ta gabatar da sabon kociyanta, Usman Abdallah ranar Talata, wanda zai ja ragamar ƙungiyar kan yarjejeniyar kaka biyu da cewar za a tsawaita masa wata 12 idan ya taka rawar gani.
Ƙungiyar da ake kira Sai Masu Gida wadda aka kafa a 1990, ta yi fice a fannin taka leda a Najeriya da nahiyar Afirka.
Pillars ita ce kan gaba a yawan magoya baya a faɗin kasar, magoya na hakika da suke cika filin wasa na Sani Abacha, duk ranar da take buga wasa a gida.
Haka kuma dubban magoya bayanta kan bi Pillars wasannin da take yi a waje da ya hada da na Premier ko na kalubalen kasar, saboda kishin da suke yi wa ƙungiyar.
Pillars ta lashe kofin Premier na Najeria huɗu da na kalubale biyu, wadda ta wakilci kasar a kofin Afirka na Champions League da Confederation Cup.
Pillars kan taka rawar gani a gasar Premier ta Nageriya, musamman karawa da Enyimba da Rangers da National da dai sauransu.
To sai dai ƙungiyar ta ci karo da koma baya, wadda rabon da ta ɗauki kofin Premier tun 2014, amma ta lashe FA Cup a 2019, wadda rabon da wata ƙungiya a Kano ta lashe shi tun 1953.
Haka kuma rabon da Sai Masu Gida ta buga gasar Afirka tun 2020, wadda aka yi waje da ita a zagayen neman shiga wasannin.
Pillars ta ci karo da matsaloli da yawa da ya kassara ƙwazon ƙungiyar tun daga rashin bayar da ƙudi a lokacin da ya dace daga gwamnati.
Wasu matsalolin ana danganta su da rashin ɗaukar ƴan wasan da suka dace da rashin ƙwazon ƴan wasa da yawan tarzoma daga magoya a gida da dai sauransu.
A kakar 2020/2021 aka ci tarar Kano Pillars naiara miliyan bakwai da dubu dari biyar, bayan da aka samu ƙungiyar da karya dokar hukumar gasar kasar da ta NFF.
Dokar ta kunshi hana nuna wasa kai tsaye a talabijin da tayar da hatsaniya daga ƴan kallo a karawa tsakanin Akwa da Pillars.
An tashi wasan ba ci, wanda aka karasa fafatawar washe gari.
Pillars ta faɗi daga gasar Premier ta kasar ranar 16 ga watan Yulin 2022, bayan matsalolin da suka baibaye ta.
Pillars ta fuskanci hukuncin masu gudanar da gasar Premier ta Najeriya, bayan da aka samu shugabanta Surajo Janbul a karawa da Dakkada.
A 2019 gwamnatin jihar kano ta sanar da naɗa Surajo Sha'aibu Yahaya da ake kira Jambul, wanda ya maye gurbin Alhaji Tukur Babangida.
Jambul ya karbi ragama lokacin da Pillars ke daf da lashe Federation Cup da kuma ta biyu a babbar gasar tamaula ta kasar.
To sai dai a kakar aka yi waje da Pillars a CAF Champions League a wasannin cike gurbi, inda Asante Kotoko ta Ghana ta ci 5-2 gida da waje.
Haka kuma a kakar gaba aka yi waje da Pillars dagga CAF Confederation Cup, inda wata karamar ƙungitya daga Senegal ta yi nasara 3-1 gida da waje.
sakamakon hatsaniyar da magoya bayan Pillrs ke yi a yayin tamaula ya sa ƙungiyar aka ɗauke ta daga buga karawa a Sani Abacha, hakan ya sa ta je filaye hudu daga wajen kasar.
An mayar da Pillar buga wasa a Ahmadu Bello daga nan ta koma filin Muhammadu Dikko a Katsina.
A Katsina ma an samu hatsaniya, inda aka mayar da ƙungiyar buga wasanninta babban birnin tarayya Abuja, kafin daga baya ta koma Sani Abacha sitadiya.
Bayan da Pillars ta dawo gida sai ta tsinci kanta a kasa-kasan teburi daga nan aka fara cuku-cukun yadda ƙungiyar za ta ci gaba da zama a Premier League.
Daga nan ne hankalin magoya baya ya tashi kan yadda Pillars ta tsinci kanta a halin kaka-ni-kayi, wadanda suka zargi shugabanta da rashin ƙwarewa.
Matsin da Jambul ya fuskanta daga wajen magoya baya ya sa ya ɗauki doka a hannunsa, lokacin da ƙungiyar ke ɓarar da maki a gida.
Lokacin da Pillars ke buga mako na 31 da Dakkada a gida, kuma masu gida na cin ƙwallo ɗaya, sai Dakkada ta farke daf da za a tashi daga wasan.
Daga nan ne Jambul ya shiga fili da cin zarafin mataimakin alkalin wasa da bukatar a soke ƙwallon da aka ci Pillars.
Hakan ya harzuka masu gudanar da Premier, waɗanda suka kori Jambul daga baya suka ce za su ɗauki matakin sha'ria a kansa.
Pillars ta karkare a mataki na 19 da maki 45 a kakar, bayan da ta ci wasa tara da canjaras tara aka doke ta karawa 20.
Haka kuma an zura kwallo 50 a ragar Pillars, ita kuma ta ci 26 a kakar bana da hakan ya sa ta yi ban kwana da babbar gasar tamaula ta Najeriya da aka karkare.
Bayan da Gwamnatin jihar Kano ta sallami Surajo Shu'aibu Yahaya, sai ta naɗa Alhaji Ibrahim Galadima a matakin riƙon ƙwarya.
Daga nan ne Pillars ta naɗa Babangida Little a matakin sabon shugaban ƙungiyar, wanda hakan ba ta canja jani ba, kan kalubalen da ƙungiyar ke fuskanta.
Shima ya yi fama da ta sa matsalolin da yawa, har da ɗaukar sabon koci Offor Paul, wanda ya yi kwana 19 aka maye gurbinsa da Usman Abdallah.
Pillars ta sallami Audu Mai Kaba kafin kammala kakar bara, bayan da ta dakatar da shi ta kuma naɗa Ahmed Garba Yaro-Yaro a matakin riƙon kwarya.
Pillars ta kare a mataki na 11 a kakar da ta wuce bayan karawa 38, wadda ba ta samu gurbin wakiltar kasar ba a gasar Afiirka a bana.
Pillars za ta fara buga Premier ta Nageriya ta bana da Ikorodu a Sani Abacha a kakar 2024/25.
Nasarorin da Kano Pillarrs ta yi a fannin tamaula
Kofin Premier na Najeriya
Guda 4: 2007–08, 2011–12, 2013, 2014.
Ta biyu a teburin Premier ta Najeriya : 2009–10.
Nigerian FA Cup
Guda 2: 2019, 1953
Ta yi ta biyu sau biyu: 1991, 2018.
Nigerian super cup.
Guda ɗaya: 2008.
Rawar da ta taka a gasar kofin Afirka
Ta halarci gasar kofin Afirka shida:
2009 – Wasan daf da karshe
2011 – Zagayen farko
2013 – Zagayen farko
2014 – Wasan cike gurbi
2015 – Zagayen farko
2020 – Wasan cike gurbi
Shin wane ne Usman Abdalla, sabon kociyan Kano Pillars
Usman Abdalla ya taka leda a gida da kuma Afirka kafin Turai, wanda ya fara daga Sanka Vipers ta Kano.
Ya kuma yi UNTL ta Kaduna da Rocks ta Kaduna da Stationery Stores ta Lagas da kuma Mogas 90 ta Jamhuriyar Benin.
Ya kuma taka leda a Kano State academic da wakilatr jihar a wasannin kasa da ake kira festival a 1980 dawakiltar Najeriya ta matasa ƴan kasa da 220 zuwa 223 tare da ɗan uwansa – Hassan Abd'Allah.
A 1991 ya koma Al Arabic da Bayer Leverkusen, ya kuma je Singapore, inda ya taka leda a Jurong FC da Khalsa FC da kuma Gombak United FC.
Abdallah ya yi ritaya daga taka leda a 2006.
Ya fara aikin horar da tamaula a Faransa da EPS FC da FC Sete da FC Frontignan da kuma Bollene FC, bayan da ya mallaki lasisin horarwa daga Turai a Ingila.
Ya kuma halarci sanin makamar aikin kociyan ƙungiyoyin Afirka da hukumar ƙwallon kafar Afirka.
Ya horar da Enyimba da lashe kofin Premier Najeriya a ƙungiyar da taka rawar gani a gasar Afirka ta Champions League.
Kafin ya karɓi aikin kociyan Enyimba ya yi mataimaki a Pillars da jan ragamar karamar ƙungiyar sai masu gida.
Tun farko ya je Enyimba a matakin mataimakin Paul Aigbogun daga baya aka bashi ragamar jan ƙungiyar, wanda ya kai daf da karshe a Champions League.
Haka kuma ya horar da Wikki Tourist ta garin Bauchi da Katsina United daga nan ya je hutu, yanzu kuma Pillars ta dawo da shi fagen fama.