Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano Pillars ta sallami koci Offor Paul
Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars ta sanar da korar koci, Offor Paul ta kuma ce ta yi haka ne da ƙyaƙƙyawar niya.
Sanarwar ta fito daga sabon shugaban riƙon ƙwarya, Alhaji Ali Muhammad Umar ta hannun ofishin yaɗa labaran ƙungiyar.
Tsohon shugaban Pillars Babangida Little ne ya ɗauki Paul a matakin riƙon ƙwarya kan yarjejeniya kakar daya a baya-bayan nan.
Ta kuma ɗauki Paul ne bayan da ta raba gari da kociyanta, Audu Mai Kaba.
Ƙungiyar da ake kira sai masu gida ta gode wa Paul kan yadda ya bayar da gudunmuwa a ƙungiyar a ɗan karamin lokacin da ya yi.
Sabbin shugabannin Kano Pillars na shirye-shiryen naɗa sabon kociyan da zai ja ragamr ƙungiyar, domin tunkarar kakar bana.
Za a fara babbar gasar tamaula ta Najeriya a karshen watan Agusta, inda Pillars za ta fara da karɓar baƙuncin Ikorodu FC ranar 7 ga watan Satumba.
Tun kan nan za a fara wasan buɗe labulen kakar 2024/25 da karawa tsakanin Enugu Rangers da El-Kanemi Warriors.
Rangers ce ta lashe kofin Premier na Najeriya a kakar da ta wuce, El-Kanemi ce ta ɗauki kofin ƙalubalen kasar, wadda ta koma buga babbar gasar a bara daga rukuni na biyu.
Pillars ta kare a mataki na 11 a bara a gasar ta Premier ta Najeriya.
A karshen makon da ya gabata gwamnatin jihar Kano ta sanar da naɗa sabbin shugabannin Kano Pillars, waɗanda za su yi aikin riƙon ƙwarya na kaka ɗaya.