AC Milan na son Hojlund, Martinez zai bar Barcelona

Ɗanwasan baya na Spain da Barcelona Inigo Martinez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Bayern Munich ta tuntuɓi Chelsea kan ɗanwasan Senegal mai shekara 24 Nicolas Jackson, wanda Chelsea ke son fam miliyan 48, kuma Newcastle United na farautarsa. (Sky Sports Germany)

Ɗanwasan gaba na Newcastle Alexander Isak ba zai buga wasannin share fage ba da ƙungiyarsa za ta fafata da Espanyol da Atletico Madrid a ƙarshen mako sakamakon rashin tabbas kan makomarsa musamman buƙatarsa da Liverpool ke yi. (Mail - subscription required)

AC Milan na son ɗauko Rasmus Hojlund daga Manchester United. Darajar ɗanwasan ta kai fam miliyan 30 amma Milan na son aro ne. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Como ta yi watsi da tayin Tottenham na fam miliyan 30 kan ɗanwasan tsakiya na Argentina Nico Paz wanda farashinsa ya kai fam miliyan 52. (Sky Sports Italia)

Aston Villa ta yi watsi da tayin fam miliyan 18 da Everton ta yi kan ɗanwasan tsakiya na Scotland John McGinn, mai shekara 30, wanda kuma Newcastle ta nuna buƙata. (Sky Sports News)

Al-Nassr ta Saudiyya na shirin biyan Brentford kuɗin da ta nema kan ɗanwasan Jamhuriyyar Congo mai shekara 28 Yoane Wissa, wanda Newcastle da Tottenham ke farauta. (L'Equipe - in French)

Ɗanwasan baya na Spain Inigo Martinez, mai shekara 34, na shirin soke kwangilar shi da Barcelona domin komawa Al-Nassr. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Manchester City ta yi watsi da tayin Roma kan ɗanwasan tsakiya na Argentina Claudio Echeverri, mai shekara 19, yayin da take son ba Girona aron ɗanwasan (Calciomercato - in Italian)