Real Madrid na zawarcin Huijsen, Al Nassr na son Magalhaes

.
Bayanan hoto, ,
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid za ta kara kaimi wajen sayen dan wasan baya, Dean Huijsen mai shekaru 19 daga Bournemouth a bazarar nan bayan da aka kara masa girma zuwa tawagar manyan 'yan wasan Sfaniya.(Sun), external

Bournemouth ce ke kan gaba a rige- rigen dauko golan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 26, daga Liverpool. (Talksport), external

Kungiyar kwallon kafa ta Al- Nassr ta Saudiyya na shirin gabatar da tayin bazara kan dan wasan tsakiyar baya na Arsenal da Brazil Gabriel Magalhaes,mai shekara 27. (GiveMeSport), external

Newcastle United na shirin sabunta kwantiragin da zai sa dan wasa mai kai hari na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya kusan ninka albashinsa . (GiveMeSport), external

Sabon darekatan wasanni na Arsenal ,Andrea Berta na son dauko dan wasa gaban Wolves da Brazil Matheus Cunha mai shekara 25 , wanda za a iya sakinsa kan fam miliyan 62.5m. (Teamtalk), external

Dan wasan tskiya na Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 22, a shirye yake ya koma Manchester City a wannan bazara yayin da ake nuna damuwa game da makomarsa a tawagar Real Madrid. (Football Insider), external

Kociyan Aston Villa Unai Emery na son kungiyarsa ta dauko dan wasan gaban Sfaniya Marco Asensio, mai shekara 29, a matsayin dan wasa na din din bayan da aka bada shi aro daga Paris St-Germain. (GiveMeSport), external

Arsenal na bibiyar kwantiragin dan wasan gefe na Bayern Munich Leroy Sane yayin da dan wasan Jamus mai shekara 29 zai iya zuwa wata kungiya a wannan bazara. (Football Insider), external

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Napoli za ta yi kokarin cimma matsaya da dan wasa mai kai hari na Denmark Rasmus Hojlund a wannan bazara , sai dai ba za ta iya biyan Manchester United farashin fam miliyan 50 da take so ba . (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 19, na cikin 'yan wasa da Manchster United ke son ta sayar a wannan bazara domin bunkasa kasafin kudinta (Florian Plettenberg), external

Tottenham na cikin kungiyoyin da ke sha'awar dan wasan tsakiya na Inter Miami da Amurka Benjamin Cremaschi mai shekara 21 , wanda ake ganin ya na burge Lionel Messi . (Teamtalk), external

Barcelona ta na son ta sayar da Ansu Fati a wannan bazara duk da cewa dan wasan gefen Sfaniya mai shekara 22, ya yi watsi da tayi akalla hudu a watan Janairu. (Fabrizio Romano), external

Manchester United na cikin kungiyoyin firimiya da ke zawarcin dan wasan tsakiya na Sunderland Jobe Bellingham mai shekara 19. (Teamtalk), external

Crystal Palace ta fara shirin dauko dan wasa mai kai hari na Ingila da Middlesbrough Hayden Hackney mai shekara 22 a wannan bazara (Football Insider), external