Arsenal ta samu ƙwarin gwiwa bayan da Merino ya koma atisaye

Asalin hoton, Getty Images
Mikel Merino ya karawa Arsenal ƙwarin gwiwa, sakamakon da ya koma atisaye kwana ɗaya tsakani da za ta fuskanci Paris St German ranar Talata.
Arsenal za ta karɓi bakuncin PSG a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League a Emirates.
Tun farko an yi ta tantama ko Merino zai samu buga karawar ta ranar Talata, saboda bai yi wasan da Arsenal ta tashi 2-2 da Crystal Palace kwana shida da ya wuce ba.
Bayan tashi a wasan Premier da Palace a Emirates, Mikel Arteta ya ce ba shi da tabbas ko ɗan wasan tawagar Sifaniya zai fuskanci ƙungiyar Faransa a Champions League.
Sai dai yanzu Arsenal ta kara samun ƙwarin gwiwa, bayan da aka yi atisaye da Merino ranar Litinin a filin Gunners na London Colney.
Sai dai watakila Arsenal za ta yi amfani da Merino a gurbin masu buga tsakiya a wasan da PSG, saboda Thomas Partey ba zai yi ba.
Kenan Leandro Trossard ne zai buga gurbin mai cin ƙwallaye, wanda ya zura huɗu a raga a wasa huɗu baya da ya yi wwa Gunners.
Haka shima Ben White ya motsa jiki ranar Litinin, wanda bai buga wa Arsenal wasan da ta kara da Palace ba a Premier Leagu, sai dai har yanzu Riccardo Calafiori na jinya. remains
Arsenal ta kawo matakin daf da karshe a Champions League a bana, sakamakon fitar da Real Madrid da cin 5-1 gida da waje zagayen kwata fainal.
Ita kuwa PSG ta fitar da Aston Villa ne, hakan ya sa ta kai gurbin daf da karshe a babbar gasar zakarun Turai.
Arsenal da PSG ba wadda ta taɓa lashe Champions League a tarihi.











