Chelsea ta ce Palmer ba na sayarwa bane, Arteta na fatan zama kocin Ingila

Asalin hoton, ARSENAL
Newcastle na son dauko Marc Guehi a watan Janairu, Chelsea za ta yi watsi da duk wani tayin Cole Palmer, Manchester City za ta kara da Bayern Munich kan Florian Wirtz.
Newcastle ta shirya tsaf don fara wani sabon yunkuri na sayan dan wasan bayan Ingila da Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 24, a watan Janairu kan kudi kusan fam miliyan 80. (Teamtalk)
Chelsea ba za ta karbi duk wani tayi kan dan wasan tsakiyarta Cole Palmer, mai shekara 22 ba, yayin da wasu rahotanni ke alakanta dan wasan na Ingila da tsohuwar kungiyarsa ta Manchester City. (Football Insider)
Har ila yau Manchester City na nuna matukar sha'awar dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, mai shekara 21, amma suna fuskantar hamayya daga Bayern Munich. (Sky Germany)
Zakarun Faransa Paris St-Germain da Real Madrid suma suna zawarcin Wirtz, sai dai Liverkusen din ta fi son dan wasan ya ci gaba da zama a Jamus. (Goal)
Manchester United na sha'awar daukar kocin Sporting Lisbon, mai shekara 39, Ruben Amorim (Florian Plettenberg)
Dan wasan Bayern Munich dan kasar Jamus Leroy Sane, mai shekara 28, ba ya sha'awar komawa Newcastle United. (CaughtOffside)
Kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes ya shirya barin kungiyar a bazarar da ta gabata kafin kungiyar ta yi masa gwaggwaban tayin sabunta kwantaragi a (ESPN)
Kociyan Arsenal Mikel Arteta, mai shekara 42, ya ce zai yi shirin jagorantar Ingila nan gaba. (Guardian)
Tottenham na sa ido sosai kan dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jamie Bynoe-Gittens mai shekara 20 (Football Insider)
Liverpool na shirin yin hamayya da Borussia Dortmund kan sayen dan wasan Red Star Belgrade da Serbia Andrija Maksimovic, mai shekara 17. (CaughtOffside)
Manchester City na ci gaba da tattaunawa don dauko dan wasan Jamhuriyar Ireland na kasa da shekaru 17 Michael Noonan, mai shekara 16, daga St Patrick's Athletic. (Fabrizio Romano)












