Arsenal na sa rai Saliba ba zai tafi ba, kocin Stuttgart ya ce wa Man U a kai kasuwa

William Saliba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na sa rai William Saliba zai ci gaba da zama a kulob ɗin, Juventus na iya shiga neman Dominic Calvert-Lewin a bazara, kocin Stuttgart Sebastian Hoeness ya ce wa Manchester United a kai kasuwa.

Arsenal na da ƙwarin gwiwar cewa ɗan bayan Faransa William Saliba, mai shekara 23, zai ci gaba da zama a Emirates Stadium duk da sha'awar da Real Madrid ke nunawa a kansa. (Express)

Juventus na iya miƙa tayinta kan ɗan wasan gaban Everton na Ingila mai shekara 27 Dominic Calvert-Lewin, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara mai zuwa. (Corriere dello Sport)

Manchester United ta tuntuɓi kocin Stuttgart Sebastian Hoeness, mai shekara 42, don maye gurbin Erik ten Hag da bazara, sai dai ya sa ƙafa ya shure tayin. (Bild)

Har yanzu dai Manchester United na da kyakkyawar alaƙar da za ta iya kai wa ga ɗauko tsohon kocin Chelsea da kuma Bayern Munich Thomas Tuchel, duk da yake ana danganta shi da aikin horas da Ingila. (Teamtalk)

Chelsea ta yi shigar sauri da bazara inda ta doke Bayern Munich wajen ɗauko golan Genk ɗan ƙasar Beljiyam mai shekara 19 Mike Penders, wanda zai tafi Stamford Bridge a watan Yulin shekara mai zuwa. (Fabrizio Romano)

Borussia Monchengladbach na bibiyar ɗan wasan gaban Arsenal ɗan Ingila Nathan Butler-Oyedeji, mai shekara 21. (Football Insider)

Ɗan wasan bayan Jamus Marvin Friedrich, mai shekara 28, na iya barin kulob ɗin Borussia Monchengladbach a watan Janairu. (Sky Sport Germany via Frankfurter Rundschau)

Arsenal ta bi sahun Tottenham wajen zawarcin ɗan wasan tsakiya daga Ukraine Georgi Sudakov ɗan shekara 22 daga Shakhtar Donetsk. (Caught Offside)

Barcelona da Arsenal da kuma Newcastle na sha'awar ɗauko ɗan wasan gefe na Jamus Leroy Sane mai shekara 28 daga Bayern Munich. (Ekrem Konur)