Firaminista Isra'ila ya gurfana a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Benyamin Netanyahu ya zama firaiministan Isra'ila na farko da ya gurfana a kotu kan zargin aikata manyan laifuka yana kan mulki.

Netanyahu ya shaida wa kotu a birnin Tel Aviv cewa zargin rashawa da ake masa ba shi da tushe.

Masu shigar da ƙara sun ce Netanyahu ya karɓi kyautuka masu tsada ya kuma bai wa kafafen yaɓa labarai toshiyar baki domin su riƙa yabon shi.

Firai ministan Isra'ilar ya yi ƙorafin cewa kafafen yaɗa labarai sun tsane shi saboda shi ba mai sassaucin ra'ayi ba ne.

Firaiministan ya kuma yi bayani sosai kan yadda yake kwashe tsawon lokaci yana aiki ba tare da ya samu koda minti biyar tare da matarsa ba.

Ana zargin Netanyahu da laifukan cin hanci da rashawa da zamba, da cin amana a wasu batutuwa daban-daban har uku.

Benjamin Netanyahu shi ne ke zaman firaministan Isra'ila da ya fi dadewa a kan mulki.

Mista Netanyahu ya yi ta kokarin jinkirta wannan shari'a, yana mai fakewa da yakin da Isra'ilar ke yi a Gaza da kuma matsaloli na tsaro.

To amma a yanzu alkalai sun bayar da umarnin a koma a ci gaba da shari'ar, kuma yanzu ana sa ran za ta dauki hankalinsa sosai a wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga Isra'ilar.

Shekara hudu da ta gabata ne aka fara shari'ar, kuma har yanzu Netanyahu ya tsaya tsayin-daka kan cewa shi ba abin da ya yi na saba wa doka - yana mai zargin cewa makarkashiya ce ta siyasa kawai da 'yan hamayya ke yi masa.

Masu gabatar da kara suna zarginsa da bai wa masu kafafen yada labarai cin hanci da toshiyar baki, domin yada labarai masu kyau a game da shi ko gwamnatinsa.

Sannan kuma ana zarginsa da karbar wata kyauta ko tukuici mai gwabi domin ciyar da muradun kashin kai na wani hamshakin attajirin shirya fina-finan Amurka.