Ko Amurka, Mexico da Canada za su iya manta bambancin da ke tsakaninsu a gasar Kofin Duniya?

    • Marubuci, Anthony Zurcher, Jessica Murphy da Will Grant
    • Aiko rahoto daga, Washington DC, Toronto da Mexico
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ya za ka yi idan aka gayyace ka wajen cin abinci amma kana zuwa sai ka ga mutanen da suka gayyace ka su kaure da muhawara mai zafi.

Masoya ƙwallon ƙafa da za su je kallon gasar Kofin Duniya a nahiyar arewacin Amurka - karon farko da ƙasashe uku za su kaɓi baƙuncin gasar - za su kasance tsakanin ƙasashen da suka daɗe ba sa ga maciji da juna.

Za a fafata wasannin ne a birane 16 tsakanin ƙasashen uku: Amurka, Kanada da Mexico.

Da alama dukkanin ƙasashen sun ajiye gabar da ke tsakaninsu gefe guda, bayan da shugabanninsu suka haɗu a birnin Washington D.C na Amurka, har ma suka ɗauki hoto tare da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA Gianni Infantino. Sai dai kasancewa a teburi guda na tsawon kwanaki 39 abu ne da za a zura ido domin ganin me zai faru.

Shugaban Amurka ya yi alfaharin cewa Amurka ce jagora a nahiyar. Hakan kuma na iya dagula lamura da maida hannun agogo baya a zaman tankiyar da ke tsakanin ƙasashen kan hulɗar kasuwanci, ci rani da safarar miyagun ƙwayoyi tun bayan da Trump ya dawo mulki.

Sai dai idan komai ya tafi yadda ake so, gasar Kofin Duniyar za ta iya inganta alaƙar da ke tsakaninsu.

Yadda ake zaman ɗar-ɗar kan kasuwanci, yawon buɗe ido da baraznar Trump

Mexico da Kanada, waɗanda abokan kasuwancin Amurka ne, ba za su taɓa manta cewa su ne ƙasashe na farko da Trump ya fara laftawa haraji a wa'adin mulkinsa na biyu ba.

Kanada ba ta jin daɗin yadda Trump ke yawan sukar ƙasar ba, da iƙirarin maida ita jiha ta 51 ƙarƙashin Amurka, inda ta mayar da martani ta hanyar cire duk wasu barasa na Amurka daga kantunan ƙasar, kuma ƴan Kanada suka daina kudanci, lamarin da ya fusata Amurkar.

Matsalar da Kanada da Mexico suka samu da Amurka ya shafi dangantakar su, in ji Carlo Dade, darakta a cibiyar hulɗar ƙasa da ƙasa ta jami'ar Calgary.

An zargi Kanada da yin zagon ƙasa ga Mexico a lokacin da Trump ke neman wa'adi na biyu, inda hukumomin Amurka da Kanada suka yi zargin Mexico da buɗe dama ga China ta samu gindin zama a Arewacin Amurka.

"Hakan rashin ɗa'a ne," in ji Dade.

Hakan ta sa Firaministan Kanada Mark Carney yake ta ƙoƙarin sake ƙulla alaƙa da Mexico, domin ganin ƙasarsa ta faɗaɗa alaƙarta fiye da Amurka.

Shin ƙasashe uku sun yi yawa?

Ba a taɓa buga gasar Kofin Duniya a ƙasashe uku a lokaci guda ba. Amma tun da gasar ta 2026 ta shafi nahiya guda, dole ƙarin hukumomi da dama su shigo ciki.

Za a iya samun ƙalubale wajen zirga-zirgar magoya baya, saboda yadda za su yi ta kai komo a tsakanin waɗannan ƙasashen domin kallon wasanni, kuma hakan zai iya dagula wata alaƙar, sakamakon yadda za a yi ƙoƙarin daƙile kwararar baƙin haure.

Bugu da ƙari, yanayin da Amurka ke ciki musamman saboda yaƙinta da Iran zai iya haifar da cece-ku-ce da kuma wasu matsalolin da ba a yi tsammani ba.

"Ba lallai ne a samu tabbacin kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen da suka yi haɗaka wajen karɓar baƙuncin da irin waɗannan gasa a duniya ba," in ji Lindsay Sarah Krasnoff, mataimakiyar Farfesa a fannin wasanni a jami'ar New York.

Ms. Krasnoff, ta ce gasar Kofin Duniya ta mata da ƙasashen New Zealand da Australia, suka kaɓi baƙunci a 2023 ta yi kyau, amma kuma gasar ta maza wadda Japan da Koriya ta Kudu suka karɓi baƙunci a 2002 ta fuskanci matsaloli da dama sakamakon yadda ƙasashen ke da daɗaɗɗen tarihin gaba a tsakaninsu.

Ita kanta FIFA ta bayyana ƙwarin gwiwar ta a wannan karon, inda ta ce: "wannan ne karon farko da ƙasashe uku da suka haɗa nahiya guda suke magana da murya ɗaya: 'Mun haɗa kai domin tabbatar da gasar Kofin Duniya mafi girma, mafi kyau da ƙayatarwa da FIFA ta taɓa gudanarwa.'"

Za a yi ƙoƙarin ɓoye kura-kurai

Shugabannin ƙasashen za su so yin amfani da wannan gasar domin nuna wa duniya cewa za su iya hulɗa da maƙotansu kuma su kunyata waɗanda ke sukar su kan lamuran da suka shafi harkokin cikin gida.

Ana nuna damuwa kan halin da babban filin jirgin saman ƙasar ke ciki, wanda ke da cunkoso da kuma halin da filin wasa na Azteca ke ciki wanda aka yi wa kwaskwarima. Har yanzu ana kuma nuna shakku kan halin da Mexco ke ciki game da miyagun ƙwayoyi inda ko a watannin da suka gabata an samu rikici tsakanin dilolin miyagun ƙwayoyi.

Ga kuma ƙungiyar malaman ƙasar na shirin shiga yajin aiki domin neman ƙarin kuɗaɗen fansho da jin daɗin ma'aikata, inda suke yunƙurin gudanar da gagarumar zanga-zanga da barazanar rufe hanyoyin zuwa filayen wasan. Taken zanga-zangar shi ne: "Idan ba a biya mana buƙatunmu ba, ba za a buga wasanni ba."

Duk da waɗannan ƙalubalen, shugabar Mexico Claudia Sheinbaum tana da ƙwarin gwiwar komai zai tafi daidai.

"Wannan lokaci ne da za a ga wasannin ƙwallon ƙafar da suka fi kowane kyau kuma za mu nuna wa duniya su wane ne mu: ba wai ƙasa ce kawai da ke al'adu ba, mutanen ƙasar suna da abubuwan ƙayatarwa da sanin ya kamata," kamar yadda ta faɗa a shekarar da ta gabata.

Ba za a iya ɓoye matsalolin da Mexico ke fuskanta ba kafin a fara wasannin nan, in ji wani ɗanjarida mai sharhin wasanni a Mexico Rafael Puente.

Ƙasashen na fatan samun nasarori baya ga gasar

Masu sharhi na ganin ƙasashen uku da ke maƙotaka na iya taɓuka abin kirki idan har suka yi abin da ya dace wajen gudanar da gasar nan da wata mai zuwa.

Ƙasashen na tsaka da nazarin yarjejeniyar kasuwanci a arewacin Amurka da aka fi sani da USMCA. Wannan na nuna rashin tabbas kan yarjejeniyar wadda ake ta duba ta tun 1994.

Mexico ta fara tattaunawa da Amurka, amma Kanada ba ta fara ba.

Kanada na ƙoƙarin inganta alaƙar kasuwanci da China, inda Mexico ta ƙara haraji kan kayayyakin China, tana ɗaukar wasu matakai game da matakin gwamnatin Trump na maida hankalinsa kan China, a cewar Dade ta jami'ar Calgary.

Amma gasar Kofin Duniya ta kawo wata dama ta diflomasiyya, kamar yadda muka ga Trump, Carney da Claudia Sheinbaum ta Mexico na fara'a da juna a yayin raba jadawalin gasar.

"Haɗa shugabannin waje guda abu ne mai kyau," in ji Dade.

Shi kuma Trump da yake ta alfaharin cewa ƙasarsa ce "jagaba" a duniya, yana ganin gasar Kofin Duniya a matsayin wata dama da Amurka za ta ƙara ɗora kanta a idon duniya.

Burinshi shi ne ya mamaye duk wata tattaunawa, ta hanyar halartar taruka ko kuma wallafa saƙonni a shafinsa na Truth Social, wanda kuma hakan zai iya raba kan maƙotan Amurkar da kuma lalata alaƙar arewacin Amurka.

Amma yana da muhimmiyar rawar takawa domin tabbatar da nasarar gasar, kuma ba zai bari a samu matsalar diflomasiyya da za ta iya kawo tsaiko ba.