Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benjamin Netanyahu: Firai Ministan Isra'ila zai fuskanci tuhuma kan cin hanci
Ministan shari'ar Isra'ila yana so a tuhumi Benjamin Netanyahu da cin hanci da zamba da cin amana.
Avichai Mandelblit ya ce Mr Netanyahu zai fuskanci tuhume-tuhumen da suka shafi cin hanci da zamba da cin amana masu alaka da laifuka uku, kafin a gama sauraron kara ta karshe.
Ana zargin firai ministan da karbar na goro daga wasu attajirai da kuma yin alfarma don jan hankalin 'yan jarida su dinga yin rahotanni masu kyau a kansa.
Mr Netanyahu, wanda zai fafata a zabe a watan Afrilu, ya musanta aikata ba daidai ba.
Ya ce ana yi masa bi-ta-da-kulli ne don kokarin kayar da shi a zaben da ke gabatowa ranar 9 ga watan Afrilu.
Ana sa ran zai gabatar da jawabi da misalin karfe takwas na dare agogon kasar.
Firai ministan zai samu damar gabatar da korafinsa kan zarge-zargen da ake masa a wajen sauraron karar na karshe, wanda ake sa ran za a yi bayan zaben.
Idan har aka ki amincewa da hujjojinsa, zai zamo karo na farko da wani Firai minista da ke kan karaga zai fuskanci tuhuma kan aikata laifuka.
Wadanne tuhume-tuhume zai fuskanta?
Mr Netanyahu zai shirya fuskantar tuhumar zamba da cin amana wajen karbar na goro - da suka hada da barasa masu tsada da zinarai - daga masu shirya fina-finai.
Ana zargin yana karbar su ne don taimakawa mutane wajen samun bizar Amurka da kaucewa biyan haraji.
A wasu laifukan biyu daban, ana zarginsa da kokarin jan hankalin 'yan jarida su dinga yin rahotanni masu kyau a kansa.
Ministan shari'ar ya ce yana ganin za a tuhumi Firai ministan ne kan zamba da cin amana da kuma cin hanci.
Wanne irin martani ake mayarwa?
Jam'iyyun adawa sun ce babu yadda za a yi Mr Netanyahu ya ci gaba da kasancewa firai minista idan hakan ta faru.
Mr Mandelblit ya ce Kotun Kolin za ta yanke hukunci ko dole ya yi murabus.
Jam'iyya mai mulki ta Mr Netanyahu ta Likud Party ta mayar da martani da kalamai masu tsauri.
Ta kira abun da ministan shari'ar ke son yi a matsayin "cusgunawar siyasa".
"Sanarwar minsitan shari'ar da aka wallafa wata guda kafin zabukan, ba tare da bai wa firai ministan damar mayar da martani kan zarge-zargen na karya ba, abun kunya ne kuma zagon kasa ne ga zabukan," in ji Lukad.