Mai-dakin Netanyahu ta bayyana gaban kotu

An wallafa

Uwargidan Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Sara Netanyahu ta bayyana a kotu cikin birnin Kudus don amsa tuhumar aikata ba daidai ba game da yin amfani da dukiyar kasa ba bisa ka'ida ba ta hanyar ba da odar abinci.

A karkashin wata yarjejeniya, ba za a daure ta a gidan yari ba, amma sai lallai ta mayar da kudin wanda ya kama sama da dala dubu 12 kuma ta biya tarar kusan dala dubu uku.

Ko da yake ta bayyana a kotu cikin murmushi, amma wannan dadadd'iyar shari'ah ta kunyata Sara Netanyahu kuma ta sake karfafa tunanin jama'a cewa mutanen gidansu na rayuwa ta kece raini.

Tun da fari ana tuhumar Sara Netanyahu da laifin yin oda daga gidan abinci na kimanin dala dubu 100, kuma aka biya da kudin gwamnati, duk da an haramta yin hakan saboda akwai kuku a gidan fira minista.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma da ita, Sarah ta amince cewa da gangan ta yi amfani da kuskuren wani ma'aikaci. Masu gabatar da kara za su jingine babbar tuhumar da suke mata kan almundahana, amma za a rubuta bayanan ta taba aikata laifi.

A bangare guda shi ma mai gidanta Fira Minista Benjamin Netanyahu har yanzu na fuskantar tasa shari'ar, kan zargin cin hanci uku, amma ya musanta aikata ba daidai ba.

Yana fuskantar zaman sauraron bahasi gabanin fara shari'ar makwanni bayan wani babban zabe da aka kira cikin watan Satumba saboda ya gaza kafa gwamnati bayan kuri'un da aka kada masa a baya-bayan nan.