Trump ya gargaɗi Netanyahu cewa 'zai bar shi da Iran'
Donald Trump ya gargaɗi Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa nan gaba kaɗan zai iya barinsa ya je ya ƙarata da Iran matuƙar ya ci gaba da rura wutar yaƙi, kamar yadda shugaban na Amurka ya faɗa wa tashar Channel 12 ta Isra'ila a wata zantawa.
Kamfanin dillancin labaran Isra'ila ya ba da rahoto a yau Litinin cewa Netanyahu bai faɗa wa Trump game da shawararsa ta baya-bayan nan ta kai wa Iran hari a ranar Lahadi ba, har sai da lokacin ya ƙure a matakin tsarawa.
Trump ya nemi Netanyahu a ranar Lahadi ya guji kai wa Iran harin ramuwar gayya kan harin da aka wa Isra'ila bayan ta ƙaddamar da hari a Beirut, babban birnin Lebanon.
Hirar ta ƙare ne ba tare da cimma yarjejeniya ba kuma Netanyahu bai sanar da Trump ba game da shawararsa ta ƙarshe a kan batun, kamar yadda tashar Channel 12 ta ba da rahoto.
Daga bisani, Netanyahu ya sanar da Sakataren Wajen Amurka Marco Rubio cewa ya yanke shawarar kai wa iran hari. Trump ya faɗa wa tashar Channel 12 cewa ya yi ƙoƙarin "rage girman" harin.
Trump ya ja kunnen Netanyahu a kan ya guji rura wuta don kada yaƙi ya sake kacamewa da Iran, ya shaida wa tashar Channel 12: "Na faɗa wa Bibi, gwamma ka yi hattara game da abin da kake yi, saboda nan gaba kaɗan zan iya barin ka, ka je ka ƙarata da Iran."